Hukumar NYSC Ta Samu Sabon Shugaba

159

Shugaban Rundunar Sojojin kasa (Nigerian Army) laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya sauyawa manjo Janar Sulaiman Kazaure wajen aiki daga hukumar Matasa masu yiwa kasa hidima na NYSC zuwa cibiyar bayanai na rundunar.

Kakakin Rundunar, Kanal Sagir Musa ne ya bayyana haka a wani sanarwa da ya fitar da ke cewa shugaban rundunar Sojojin kasan ya yi sababbin nade-naden mukamai ga wasu manyan hafsoshin sojan kasa a wani garambawul da gyaran fuska da ya gudanar a rundunar.

Kanal Sagir Musa ya ce janar Buratai ya amince da nada birgediya janar S S Ibrahim a matsayin a matsayin sabon shugaban hukumar NYSC, bayan dauke shi daga jami’ar rundunar sojan kasa da ke Biu, a jihar Borno.

Sai sanarwan ya kara da cewa an sauyawa birgediya janar CA Bossman daga cibiyar litattafai na rundunar zuwa mukamin daraktan sashen kula da makarantun sakandaren sojoji da ke fadin kasarnan.

Sai kuma Birgediya janar E Angaye da aka nada a matsayin sabon darakta mai kuka da tsofaffin sojoji.
Bugu da kari, an canza birgediya BA Tsoho da aka canza daga hedkwatan rundunar sojan kasa zuwa cibiya koyar da harsuna na rundunar sojan kasa a matsayin babban kwamanda.

Sai kuma aka dauke birgediya janar AA Goni zuwa hedkwatan rundunar sojojin, da kuma Birgediya jaanar FC Onyeari da aka canza daga sashin sufuri a hedkwatan rundunar zuwa matsayin mukaddashin darakta mai kula da ciye-ciye da tande-tande.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan