Hukumar WHO: Kasarnan Tana Fuskantar Sake Bullowar Annobar Shan Inna

134

Hukumar lafiya ta Duniya WHO ta ce kasarnan tana daga cikin jerin kasashe tara na Nahiyar Afrika wanda annobar cutar shan Inna ya sake bullowa.

Hukumar WHO ta bayyana hakan ne a cikin waji sanarwa da ta fitar a jiya laraba ta hannun mai magana da yawun hukumar na Nahiyar Afirka, mista Collins Boakye-Agyemang.

Hukumar ta ce sake bulliwar cutar wani babban abin damuwabga duniya baki daya da ya ke bukatar daukan mataki da gaggawa ga kasashen domin tabbatar da cewa anyi wa yara riga kafin cutar don samar da kariya.

Sauran kasashen da hukumar ta lissafa sun hada da Chad, da Cameroon, da Jamhuriyyar Dimokaradiyyar Kongo, da Liberia, da Guinea, da Madagascar, da Mali, sai Uganda.

Sanarwan ya ce Kasashe a nahiyar Afirka suna Fuskanci dawowar cutar a watanni 12 da suka gabata musamman kasar Madagascar wanda annobar ya fi kamari don ya shafi sama da mutane 122,000 tsakanin watan Oktoban bara zuwa watan Afrilun da muke ciki.

Kamfanin Dillancin Na Kasa (NAN) ya rawaito cewa cutar shan Inna cuta ce da ke saurin yaduwa cikin al’umma kuma idan aka yi riga kafi yana hana mutuwar yara yan kasa da shekaru biyar.

Kamfanin NAN ta ce a lokacin da ake kaddamar da satin riga kafi na Nahiyar Afirka karo na Tara, a ranar laraba a Kasar Sào Tomè and Principe kungiyoyi da masu ruwa da tsaki akan harkar riga kafi sun jaddada muhimmancin yin riga kafin domin kare rayuka da inganta lafiyar al’umma.

Satin na riga kafi da yake gudana daga ranar 22 zuwa 28 na watannan a wurin taron kungiyoyin sun yabawa mutanen da suka jajirce wajen bada gudunmawa don fadada wuraren da ake zuwa yiwa al’umma riga kafi a Afirka musamman Iyaye, da Masu Uguwanni, da ma’aikatan lafiya.

A karshe, sun yi kira ga al’umma da su bada hadin kai ga ci gaba da gudanar da riga kafi ga ýaýansu don samu kariya daga cututtuka.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan