JAMB ta sa ranar da za ta saki sakamakon jarrabawa

186

Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Makarantu, JAMB ta tabbatar wa da ɗaliban da suka zana Jarrabawar Bai Ɗaya ta Shiga Manyan Makarantu, UTME cewa za a saki sakamakon jarrabawar daga ranar 29 ga watan Afrilu, 2019.

Shugaban Sashin Yaɗa Labarai na JAMB, Dakta Fabian Benjamin ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN ranar Asabar a Bwari, Abuja.

Mista Benjamin ya ce nan gaba kaɗan za a gama tantance sakamakon, kuma a sake shi.

“Har yanzu muna kan tantancewa, amma muna fata, kowane lokaci daga mako mai zuwa, sakamakon zai kammala”, in ji shi.

Da yake jawabi game da shirin Hukumar na tantance ɗaliban da suka zana jarabawar ta UTME daga shekarar 2009 zuwa 2018, Mista Benjamin ya ce za a fara tantancewar ne bayan sakin sakamakon 2019.

Ya ce wannan yana daga yunƙurin Hukumar na warware matsalolin satar amsa a tsarin gudanar da jarrabawar.

Dama tuni Hukumar ta ce za ta saki sakamakon jarrabawar 2019 ne kaɗai bayan gudanar da zuzzurfan bincike don gano tare da kama masu maguɗin jarrabawa.

Tantancewar za ta gano waɗanda suka yi rijista fiye da sau ɗaya, ta hanyar ɗaukar hoton yatsa, za kuma ta yi maganin rijistar gungu-gungu da wasu makarantun masu faɗa a ji suka yi, waɗanda daga ƙarshe suke cakuɗa bayanan ɗalibai.

“Yadda aka saba, ana sa ran sakamako ya fito cikin sa’o’i 24 zuwa 48, kamar yadda aka yi a jarrabawar da suka gabata a 2017 da 2018.

“Amma, Hukumar ba ta so hakan ya ƙara maimaituwa.

“Wannan shi ya jawo shirin jinkirin, wanda wani ɓangare ne na yunƙurin da ta yi tana sane don tsaftace, ta gano ta kuma warware dukkan matsalolin maguɗin jarrabawa.

“Hukumar za ta ci gaba da yin hukunci na ba-sani-ba-sabo ga duk wani maguɗi da ta gano ko da bayan an saki sakamako ne.

“Amma Hukumar ta wajabta wa kanta tantance dukkan aikace-aikace a dukkan cibiyoyi ta hanyar ɗaukar bayanai da na’urorin ɗaukar hoto na CCTV, don tabbatar da cewa ba ta saki sakamakon jarrabawar da yake da alamar tambaya ba”, in ji JAMB.

JAMB ta ce kafin ta sanar da sakamakon a hukumance, dukkan ɗalibai za su iya aikawa da RESULT ta hanyar rubutaccen saƙo zuwa 55019, da lambar wayar da aka yi amfani da ita wajen yin rijista.

Ta ce, sakamakon zai zo jim kaɗan ta rubutaccen saƙo.

Hukumar ta ce an sauƙaƙa wannan hanyar duba sakamakon ne don kawar da tatsar kuɗi da masu cibiyoyin kasuwanci da masu shagunan Intanet ke yi, waɗanda yawanci kan cuci ɗalibai.

Ta yi kira ga ɗalibai da su yi watsi da dukkan wasu saƙonni da ake yaɗawa na yadda za a duba sakamakon, saboda duk hanyoyi ne na yaudara.

An gudanar da jarrabawar UTME ne daga 11 zuwa 18 ga watan Afrilu, kuma kimanin ɗalibai miliyan biyu ne suka yi rijistar ta.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan