Akwai Banbanci Tsakanin Shaidar Haihuwa Na Hukumar Kididdiga Da Na Asibiti – Inji Hukumar Kididdiga

136

Hukumar Kididdiga ta Kasa ta ce akwai bambamci tsakanin takardar shaidar haihuwa da hukumar ke bayarwa ( Birth Certificate) da takardar shaidar haihuwa na asibiti ( certificate of live birth).

Kwamishina mai wakiltar jihar Kano a hukumar Kididdiga, Dr Sulaiman Lawal ne ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa a garin Abuja inda ya ce kowanne daga cikin wadannan takardu suna da amfani na musamman wanda ya banbanta su.

Dr Sulaiman ya yi bayani cewa takardar shaidar haihuwa na asibiti shi ne takardar da asibitoci ke bayarwa na shaidar haihuwan jariri wanda ke dauke da sunan jariri, da na Iyaye, da sunan likita, da sunan Asibiti, da jinsi, da ranar haihuwa da lokaci, da kabila, da sunan ma’aikaci mai shigar da bayanai.

Wannan takarda ana cike shi kuma a bayar da zarar anyi haihuwa a asibitoci kuma hanya ce ta shigar da yawan haihuwa a cikin kididdiga na asibitoci.
Ya kara da cewa, a bisa ka’ida, kamata ya yi asibitoci su rinka aikawa hukumar kididdiga wadannan bayanai amma har yanzu babu tanadi akan hakan.

Takardar Shaidar haihuwa na hukumar (Birth Certificate) shi ne takardar shaidar wanda hukumar Kididdiga ta ke bayarwa ga mutum domin tabbatar da shaidar haihuwarsa daga gwamnati. Takardar shaidar haihuwa yana dauke da bayanai da suka hadar da Suna, da sunan Iyaye, da ranar haihuwa, da garin haihuwa, da kasar haihuwa, da aikin Iyaye, da adireshinsu, da kabilarsu.

Dr Sulaiman Lawal ya ce don haka, takardar shaidar haihuwa na asibiti yana tabbatar da haihuwar jariri a raye yayin da takardar shaidar haihuwa na hukumar yana dauke da bayanai wanene jariri, da Iyayensa, da inda aka yi haihuwa da sauransu. Rashin wannan muhimman takarda zai iya zama matsala domin mutum bai da hanyar bayyana kanshi.
Ya kara da cewa hukumar ba zata karbi shaidar haihuwa na asibiti a madadin takardar haihuwa na hukumar.

A karshe ya ce ba dai-dai ba ne yan kasa su dinga amfani da takardar shaidar haihuwa na asibiti a madadin takardar shaidar haihuwa na hukumar. Hakan ya sa ma’aikatan hukumar suke shirye-shiryen gudanar da gangamin wayar da kai ga jama’a domin sanin muhimmancin, da kuma bambamcin wadannan takardu biyu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan