Ko kun san illar yaɗa hadisin ƙarya?

219

Hadisi shi ne madogara ta biyu da Shari’ar Muslunci take amfani ita bayan Littafin Allah, Ƙur’ani Mai Girma.

Malamai masana Hadisi sun bayyana ma’anarsa da cewa:

“Hadisi shi ne maganganun Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi), aikace-aikacensa, da kuma abubuwan da aka yi a gabansa bai hana ba”.

Al’ummar Musulmi suna matuƙar girmama Hadisan Manzon Allah (tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi) saboda kamar yadda na bayyana a gabatarwa, shi ne madogara ta biyu da Shari’ar Muslunci ke dogara da ita bayan Ƙur’ani.

Kai, wasu ayoyin Ƙur’ani ma ba a iya fahimtar su sai an koma cikin Hadisan Manzon Allah, (tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi).

Zuwan Kafafen Sada Zumunta na Zamani (Social Media a Turance) ya taimaka matuƙa gaya wajen yaɗa hadisai, sakamakon sauƙin amfani da kuma saurin da kafafen suke da shi wajen isar da saƙo.

Al’ummar Musulmai suna ilmantuwa ƙwarai da gaske ta hanyar hadisan da ake yaɗawa a Kafafen na Sada Zumunta.

Sai dai wani hanzari ba gudu ba, akwai hadisai da ake yaɗawa a waɗannan kafafen waɗanda kwata-kwata ba su tabbata daga Manzon Allah ba.

Ya zama dole masu yaɗa hadisan ƙarya a Kafafen Sada Zumunta na Zamani da ma ko’ina ne su daina, domin kuwa Manzon Allah ya faɗa a hadisin Abu Huraira, inda yake cewa:

“Duk wanda ya yi min ƙarya da gangan, to ya tanadi wajen zamansa a wuta”.

A wani hadisin makamancin wannan, Annabi yake cewa:

“Haƙiƙa yin ƙarya a gare ni ba kamar yin ƙarye ga wani ba ne. Duk wanda ya yi min ƙarya da gangan, to ya tanadi wajen zamansa a wuta”.

Mai yaɗa hadisin ƙarya babu shakka zai yi wa al’ummar Musulmi illa ba ‘yar ƙarama ba, domin za a iya dogara da hadisin da ya faɗa a yi wani aikin ibada da nufin samun lada, a ƙarshe ba za a samu ladan komai ba, sai ma akasin haka.

Wasu hadisan ƙaryar ma sai a ce Bukhari da Muslim ne suka ruwaito su.

An kuma yi imani cewa Sahih Bukhari da Sahih Muslim su ne litattafai mafiya Inganci bayan Ƙur’ani.

Shin ko masu yaɗa hadisan ƙarya na yin haka ne don a yadda da su?

Ɗaya daga cikin irin waɗannan hadisai na ƙarya shi ne hadisin da ake yaɗawa musamman idan watan Ramadan mai alfarma ya gabato.

A cikin wannan hadisi, ana cewa:

“Manzon Allah tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi ya ce, wanda ya sanar da wasu gabatowar watan Ramadan, haƙiƙa wuta ta haramta a gare shi”. (Bukhari da Muslim suka ruwaito shi).

Na tambayi Malam Hafiz Muhammad, wani malami ɗan asalin jihar Kano dake karatu a Jami’ar Azhar dake Masar, game da ingancin wadannan hadisi, sai ya ce:

“Ban san hadisin nan da wannan lafazin ba, ban san shi ba gaskiya, iya bincikena. Ka ga ko kwanan nan, duk wasu hadisai da suka shafi Ramadan ina bincike a kan su, kusan ma zan ce a cikin ‘takhrijin’ hadisi nake koyaushe.

“Amma, da za a sami wanda ya ciro hadisin daga Sahih Muslim ɗin ya ce ko Bukhari ya ruwaito ya bada ragamin hadisin, ko kuma ya kawo sahabin da ya ruwaito shi, ko kuma lafazi guda ɗaya ya kawo mana a Bukhari ɗin na yankin hadisin, za mu iya bincikawa”.

A cewar Malamin, Kafafen Sada Zumunta na Zamani sun kawo rikici-rikice a addini, yana mai cewa duk mutumin da zai riƙa ta’ammali da rubuce-rubucen Kafafen, to babu shakka zai yi wa Annabi ƙarya.

“WalLahi, ka ji na rantse maka, summa talLahi wannan hadisin babu a Bukhari babu a Muslim, babu a cikin wani littafi ingantacce na litattafan Hadisi. Hadisin ƙarya ne ba shi da asali daga Manzon Allah, kwata-kwata ko ƙanshin gaskiya babu wannan magana”, in ji Malam Hafiz.

Malamin ya ce ya tuntuɓi Majalisar Fatawa ta Duniya wadda ke da Shelkwata a Masar a kan wannan Hadisi, ya ce ya tattauna da manyan malaman duniya, su ma suka ce yanda yake jin wannan hadisi, haka su ma suke jin sa.

Malam sun ce kwata-kwata wannan ba hadisi ba ne, sun kuma yi kira ga Musulmai da su guji yaɗa shi.

Malam Hafiz ya ƙara da cewa ba irin binciken da bai yi ba don ya gano Ingancin wannan Hadisi, amma bai gano ba, ya tabbatar da cewa ƙarya aka yi wa Annabi, ba Hadisi ba ne.

Ya ƙara da cewa yana daga abinda Sahabban Manzon Allah suka tafi a kai wajen kare Sunnar Manzon Allah, shi ne neman ‘isnadin’ hadisi.

“Akwai abinda Malaman Hadisi suke cewa ‘ɗalabul isnad’. Babu yadda za a yi mutum ya kawo hadisi ya ajiye maka babu isnadi kuma ka yadda da shi.

“Akwai lokacin da ɗaya daga cikin Sahabban Manzon Allah sallalLahu alaihi wa sallam, yake gaya wa Sayyidna Umar, Sayyidna Umar ya aika a kira shi, ina tunanin Abu Musal Ash’ari ne, Sayyidna Umar ya aika a kira shi, Sayyidina Umar ya ji kamar bai zo ba, shiru-shiru bai zo ba, sai Sayyidna Umar, bayan ya zo sai ya ce tun yaushe muka aika muka ce ka zo ba ka zo ba?

“Sai ya ce na zo, na yi muku sallama sau uku sai na ji ba a buɗe min ba na ji shiru, sai na koma, saboda kuma na ji Manzon Allah ya ce idan ka yi wa mutane sallama sau uku, ka je ƙofar gida ka yi sallama sau uku, ka ji ba a amsa ba ka juya.

“Don haka, me Sayyidna Umar ya faɗa masa? Ce masa ya yi: “Aƙim alaihi bayyina” (ku tsayar masa da haddi), wannan Hadisin da ka ce min ka ji shi, ni ban taɓa jin sa ba amma ka kawo dalilinka na cewa Manzon Allah ne ya faɗi wannan Hadisin, in ba haka ba sai na sa an yi maka bulala.

“Ka gani, a cikin mutanen da Sayyidna Umar ya faɗi wannan, a ciki wani ya ce WalLahi ni na ji Manzon Allah ya faɗi wannan maganar.

“Ka ga wannan shi ake kira ‘ɗalabul isnad’. Kai tsaye da ya faɗi Hadisi ya ce ya kawo masa ‘isnad”, a cewar Malam Hafiz.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan