Hukumomi a kasar Amurka sun kama wasu yan Najeriya har mutum tara bisa laifin damfarar mutane kudade da suka kai dala miliyan 3.5
Babban alkalin shiyyar kudancin birnin New York, Geoffrey S Berman da wani babban jami’in da ke bincike akan shige da fice, da fasakauri a yankin Florida da kewaye a cikin Amurka, James C Spero su suka bayyana cafke wadannan mutane a wani sanarwa da suka fitar.
A ranar alhamis, 25 ga watan Afrilu ne jami’an kasar Amurka suka sanar da duniya kama wadannan bata gari. Su dai yan Najeriyan suna damfara mutane ne ta hanyar yaudarar su da soyayya a matsayin mace da kuna kasuwancin man-fetur a kasar Rasha na bogi.
Mista James C Spero ya bayyana sunayen yan damfarar kamar haka; Oluwaseun Adelekan wanda aka fi sani da Sean Adeleke, sai Olalekan Daramola, da Solomon Aburekhanle, da Gbenga Oyeneyim. Sauran mutane biyar da hukumar Kasar Amurka ta cafke su ne; Abiola Olajumoke, da Temitope Omotayo, da Bryan Eadie, da Albert Lucas da kuma Ademola Adebogun.
Akwai yiwuwar kowanne daga cikin yan damfarar zai iya fuskantar daurin shekaru 20, a gidan yari idan aka tabbatar da laifin da suka aikata. Babban mai shari’a na kasar Amurka, Geoffrey S Bernan ya ce wadannan mutane masu damfara sun damfari bayin Allah da basu ji ba, basu gani ba ta hanyar aika sakonnin na e-mail ta yanar gizo kamar kamfani na hakika ko kuma mace mai neman miji.