Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta sa ranar da za ta miƙa wa Shugaban Ƙasa kasafin kuɗin 2019

210

A ranar Talata ne Majalisar Wakilai ta Ƙasa ta ce ranar Alhamis mai zuwa Majalisar Dokoki ta Ƙasa za ta gabatar wa Shugaba Muhammadu Buhari kasafin kuɗin da ta amince da shi na shekara ta 2019 da ya kai triliyan 8.9.
Shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar Dokoki, Mustapha Dawaki ya sanar da haka yayinda yake yi wa manema jawabi bayan zaman Majalisar ranar Talata a Abuja.

Mista Dawaki ya bayyana cewa an samu ƙari a kasafin kuɗin da Fadar Shugaban Ƙasa ta gabatar na triliyan 8.83 sakamakon wasu ‘ayyuka na musamman’ da Majalisar Dokokin ta shigar.

Ya ce ayyukan na musamman sun haɗa da tanadin Biliyan 24.6 a matsayin alawus na barin Majalisa ga ‘yan Majalisu masu barin gado, da Biliyan 10 domin yaƙi da ta’addancin Zamfara.

Ya ce hutun Kirsimeti da babban zaɓen ƙasar nan su suka sa aka samu jinkiri wajen amincewa da kasafin kuɗin.

“Shugaban Ƙasa ya gabatar da wannan kasafin kuɗin ne ranar 18 ga watan Disamba, 2018, amma wasu abubuwa da suka sha kanmu kamar hutun Kirsimeti da na Sabuwar Shekara su ma sun shafi amincewa da Dokar Kasafin Kuɗin cikin gaggawa.

“Kuma, kar ku manta, dole mu tafi hutu don shiga zaɓukan watan Fabrairu; dukkan waɗannan abubuwa ne da suka kawo tsaiko wajen amincewa da Dokar Kasafin Kuɗin.

“Muna fata, zuwa Alhamis, za mu miƙa wa Shugaban Ƙasa kasafin kuɗin don sa hannu.
“Mun bar farashin man fetur da farashin Dala kamar yadda ɓangaren Zartarwa suka aiko”, in ji Mista Dawaki

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan