Yadda aka saki Zainab Aliyu

250

Gwamnatin Tarayya ta ce Hukumomi Saudiyya sun saki Zainab Aliyu wadda suka kama bisa zargin cewa ta shigar da muggan ƙwayoyi a ƙasar.

Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Ƙasashen Waje ya bayyana haka a wani taron manema labarai ranar Talata a Abuja.

Ya ce gwamnati ta iya tabbatar da cewa Zainab ba ta da laifi, kuma ɗan Najeriya na biyu da shi ma abin ya haɗa da shi gobe Hukumomin na Saudiyya za su sake shi, inda za su miƙa shi Ofishin Jakadancin Najeriya dake Saudiyya.

An ta yin kiraye-kiraye cewa a sake ta, inda har Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci Ministan Shari’a, AGF, Abubakar Malami da ya yi gaggawar sa baki ya kuma tabbatar da an sake ta a kan lokaci.

Biyo bayan umarnin na Shugaban Ƙasa, Mataimakiyar Shugaban Ƙasa ta Musamman Kan Harkokin ‘Yan Najeriya Mazauna Ƙasashen Ƙetare, Abike Dabiri-Erewa ta tabbatar wa ‘yan ƙasar nan cewa suna samun ci gaba sosai, kuma za a sake ta, da ita da mutane biyun da suke cikin irin wadannan hali.

Hukumomin Saudiyya sun kama Zainab, wadda ɗaliba ce a Jami’ar Maitama Sule dake Kano bayan samun ƙwayar Tramadol a jakarta.

Ta yi iƙirarin cewa saka mata ƙwayar aka yi a jakarta.

Bayan nan ne Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa, NDLEA ta gudanar da bincike, inda ta gano cewa wasu ma’aikata ne suka saka wa Zainab ƙwayar a jakarta a Filin Jirgin Saman Ƙasa da Ƙasa na Malam Aminu, MAKIA dake Kano.

Ɗalibar ta tashi ne zuwa Saudiyya ta ta MAKIA don gabatar da Umara ita da mahaifiyarta, Maryam da ‘yar uwarta, Hajara.

A yau Talata ne kuma a birnin Kano ɗalibai, waɗanda mafi yawa suka ce abokan karatun Zainab ne da sauran jama’a suka yi zanga-zanga, don yin kira ga hukumomi su yi wa Zainab adalci.

Ɗalibai sun je Gidan Gwamnatin Jihar Kanon da Ƙaramin Ofishin Jakadamcin Saudiyya dake Kano don gabatar da ƙorafin nasu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan