Hanyoyin Shiryawa Watan Ramadan Domin Samun Falala da Rahamar da ke Ciki

138

A yayin da ya rage saura kwanaki kadan kafin shigowar watan mai falala da albarka, watan azumin Ramadan, yana da kyau kowanni musulmi ya shirya domin samun gafara da rahamar Allah SWT a cikin wannan wata mai daraja.

Kamar sauran shika-shikan addinin Musulunci, azumin watan Ramadan ya wajaba a kan kowanni musulmi balagagge, mai lafiya da ya ke raye a wannan lokaci, wanda bai da wani uzuri da shari’a ta amince da shi domin ajiye azumin. Don haka ya ke da matukar muhimmanci mutum ya shirya yin wannan ibada mai girma da dimbin falala.

 1. Kirgan wata:- Yana da kyau mutum ya kasance mai kirgan wata domin sanin yaushe watan Sha’aban zai kare kuma yaushe a ke sa ran kamawan watan Ramadan. Yin hakantare da iyalai ko abokai zai sa mutum ya fara shiryawa watan ta hanyar tattaunawa a kan kirgan watan.
 2. Sanin watan Ramadan :- Yana taimakawa matuka idan mutum ya nemi sani a kan watan Ramadan ta hanyar karanta littattafai a kan hakan, ko sauran karatuttuka ko a yanar gizo domin sanin falalar watan, da hanyoyin da za a bi domin samun falalar.
 3. Yin tanadi a kan watan:- Yana da kyau duk mususlmi ya zauna ya fitar da wani tanadi ko tsari na ibadu da saura aiyuka na samun lada a cikin watan Ramadan kamar saukan karatun Al-Kur’ani, yin Sallah na Asham ko Taraweeh, gayyata ko ziyartar yan uwa domin shan ruwa. Yana da kyau mutum ya fitar da tsari da zai taimaka masa ya yi ibadu a watan.
 4. Sanin Tsarin Rayuwa:- Kafin mutum ya iya fitar da tsarin a zai taimaka masa wajen yin ibada a watan Ramadan, yana da kyau mutum ya yi duba ga tsarin rayuwarsa. Ka duba yanayin rayuwarka na yau da kullum, menene ya kamata ka rage saboda samun damar yin ibada a watan Ramadan, me zaka daina yi baki daya, sannan kuma me zaka kara himma wajen yi. Ya zaka cigaba da gudanar da rayuwarka ba tare da ibadu a watan Ramadan sun shafi aiyuka na yau da kullum ba. Wadannan da sauransu na daga cikin abubuwan dubawa.
 5. Shirya Ruhi domin yin Ibada:- A mafi yawancin lokaci mukan manta cewa Dan Adam ya ginu a bisa abubuwa uku ne, watau Gangan jiki, Ruhi da Rai (Body, Soul & Mind). Don haka da rai da ruhi suna bukatar su zama a shirye domin samun falala a watan Ramadan. Hakan na yiwuwa ta wadannan matakai :
  • Yawaita yin addu’a a kullum don samun riskar watan cikin koshin lafiya da samun damar yin azumin.
  • Neman tuba da gafarar Allah SWT bisa laifukanka tun kafin shigowar watan Ramadan.
  • Addu’ar samun kwarin gwiwar yin azumin da sauran ibadu a watan yanda Allah SWT ya ke so kuma aiyukan su zama karbabbu.
  • Neman gafarar iyali, yan’uwa, abokan arziki, makota da duk wani wanda a ka sabawa.
  • Tsarkake zuciya daga duk wani abin ki da miyagun dabi’u da abubuwan da suka haramta.
  • Yawaita addu’a da yin aiyukan lada.
 6. Yawaita Aiyuka Na Gari:- Yana da kyau mutum ya dauki niyyar yawaita aiyuka na gari wadanda zasu kyautata halayya da dabi’unsa a watan Ramadan, sannan ya daura niyyar cigaba da aikatasu ko da watan ya wuce, misali yawaita kyauta da sadakavda taimakawa mabukata da masu rauni, kyautatawa al’umma musamman masu kusanci kamar iyali, yan’uwa, abokan arziki da makota da sauransu. Yawaita sauran aiyukan lada.
 7. Gujewa Aiyukan Assha:- Yana da kyau mutum ya raba kansa da duk wasu miyagun aiyuka da wanda zasu sa shi asaran lokaci da wanda zasu raunata ibadarsa kamar gulma, yi-da-wani, yawan bata lokaci a na kalle-kallen fina-finai ko jin wakoki, ko yawan hira ta babu gaira babu dalili a kafofin sada zumunta. Duk wadannan ya kamata mutum ya rage su matuka domin mai da hankali kan ibada.
 8. Gudanar da Shiri:- Shi ne ka tabbatar da cewa dukkan aiyukanka na rayuwa bai hana ka ibada ba, ka tabbatar da na samu dai-daito a tsakanin hidimomin rayuwa da ibadu a watan Ramadan. Ka da ka bari rayuwarka ta duniya ta rinjayi ibadun da zaka yi a wannan watan mai alfarma. Duk wani taro ko aiyuka da za a yi, ya zamto ba baya hana yin Sallah a kan lokaci ko sauran ibadu. Ya zamana cewa ibadanka a watan Ramadan ba zai hana ka aiyukan rayuwa ba. Haka nan kada shagalin rayuwa ya sa ka manta falalar watan , ciye-ciye da shaye-shaye ya hana mutum yin ibada ko kuma amfani da waya ya sa mu shagaltu. Allah Ya bamu ikon ganin wannan wata mai alfarma, ya sa mu yi ibada, sannan ibadun mu su zama karbabbu, Ameen.
Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan