Kasar Mozambique Na Bukatar Agaji Cikin Gaggawa Inji Kungiyar Save The Children.

191

Wata kungiya mai suna Save The Children ta yi kira ga al’umma da akai agaji cikin gaggawa ga mutane a kasar Mozambique wanda guguwar Kenneth da ta rutsa da su.

Guguwar da ake kira da Cyclone Kenneth ya afku ne biyo bayan ruwan sama mai karfi da Iska, wanda ya janyo ambaliyar, da zaftarewar Kasa da guguwa mai karfi da ya shafe kauyuka da rusa gidaje sama da 1000 a satin da ya gabata a Arewacin kasar.

Hukumar Kula da Annoba ta Kasar (Mozambique’s National Disaster Managemnt Institute) ta ce zuwa yanzu mutum 38 ne suka rasa rayukansu a sai wasu mutum hudu daga Comoros Islam a sanadiyyar guguwar Kenneth.

Sannan kuma, gidaje da sauren gine-gine da suka hadar da makarantu, asibitoci da sauransu guda 3000 suka rushe, yayin da guda 32,000 kuma bangarorinsu suka rushe, sai Gonaki da fadin su ya kai hekta 30,000 ya lalace.

Bugu da kari, majalisar Dinkin Duniya Karkashin Ofishin Kula da al’amuran al’umma ( United Nations Office for the Co’ordination of Humanitarian Affairs) a ranar 29 ga watan Afrilu sun ce mutum dubu 20,720 suka yi gudun hijira don neman mafaka daga annobar guguwar, sannan an ceto mutum 300 da kuma wasu mutum 7,554 wanda gwamnatin Kasar ta ce suma suna cikin hatsari.

Hakan yasa kungiyoyin sa kai da na agaji irin su Save The Children, da Majalisar Dinkin Duniya suke ta kiraye-kirayen neman agaji ga wanda annobar ta shafa, domin akwai yiwuwar samun karuwar yawan wanda zasu rasa rayukan su ko kuma su shiga mawuyacin hali saboda annobar guguwar kenneth.

Baya ga haka, rahotanni sun bayyana cewa akwai yiwuwar sake faruwar guguwar kenneth a sassan arewacin kasar kuma zai iya shafar wani bangare na Comoros Island da Kasar Tanzania.

Guguwar Kenneth ta zo ne wasu satittika bayan faruwar annobar guguwar Idai da ya shafi wasu bangarorin kasashen Mozambique, da Zimbabwe, da Malawi, da Madagaskar wanda ya yi sanadin asaran rayuka da dukiyoyi da dama.

Majalisar Dinkin Duniya ta ba kasar Mozambique agajin kudi na Dala Miliyan 13 domin samar da Abinci, da tsaftacaccen ruwan sha, da gyaran ababen more rayuwa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan