Malamai Zasu Taimaka Wajen Magance Rashin Tsaro Ta Hanyar Yin Wa’azuzzuka Inji Sheikh Pantami

148

Yawan karuwar matsalolin tsaro da tabarbarewar tarbiya a kasarnan ya sa malaman addini yin kira ga shugabanni tare da mara musu baya don ganin an shawo kan lamarin.

A wani taron karawa juna sani da kungiyar Izala ta gudanar na kwanaki uku, a dakin taron makarantar kimiyya na kungiyar da ke kan titin zariya a garin Jos, a ranar lahadin da ta gabata, Sheikh Isa Pantami ya bayyana takaicinsa bisa karuwar miyagun dabi’u a cikin al’umma.

Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami ya ce yawan abubuwan batanci da ake aikatawa a kasarnan a yanzu yafi wanda aka yi shekaru 30 da suka wuce.

Shehun malamin ya ce samun karuwar aikata miyagun aiyuka da suka hadar da Sham muggan kwayoyi kamar Kodin, da sauran ababen sa maye yawan zinace-zinace, da yin luwadi, da madigo, da aikata ta’addanci irin su garkuwa da mutane don karbar kudin fansa, sace-sacen shanu da kashe masu shi, da sace matayensu ana musu fyade, abu ne da ke ciwa gwamnati tuwo a kwarya wanda ya zama wajibi malamai su mara wa shugabanni baya kan matsalolin na tsaro.

Dr Isa Pantami, wanda shi ne darakta janar na hukumar Kimiyya ta Tarayya NITDA kuma babban bako mai jawabi a taron ya kara da cewa babu abin da ya fi damun shugaba Buhari kamar matsalar rashin tsari a kasarnan, musamman a jihohin Arewacin kasarnan.

Don haka sheikh Pantami ya yi kira ga malamai da su kara jajircewa wajen yin wa’azuzzuka akan abubuwan da Allah ya haramta aikata su, da kuma irin azabar da masu aikata wadannan laifukab zasu fuskanta idan suka mutu ba tare da sun tuba, sun daina aikata su ba.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan