A ranar Alhamis da ta gabata ne Shugaba Muhammadu Buhari ya yi tafiya zuwa Birtaniya domin wata ‘ziyarar ƙashin kai’ ta kwana goma ba tare da aikawa da wasiƙa zuwa Majalisar Dokoki ta Ƙasa ba ko kuma naɗa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin Muƙaddashin Shugaban Ƙasa ba.
Abinda da Shugaban Ƙasa ya yi ya jawo muhawara game da Sashi na 145 na Kundin Tsarin Mulkin ƙasar nan wanda ya ce: “Duk lokacin da Shugaban Ƙasa zai tafi hutu, ko kuma dai ya kasa gudanar da ayyukan ofishinsa, zai tura da sanarwa a rubuce zuwa ga Shugaban Majalisar Dattijai da kuma Kakakin Majalisar Wakilai game da haka, kuma har sai ya ba sanarwa su a rubuce ne sannan Mataimakin Shugaban Ƙasa zai iya yin aiki a matsayin Muƙaddashin Shugaban Ƙasa.
Sashin ya ƙara da cewa idan Shugaban Ƙasa bai dawo ba cikin kwana 21, Majalisar Dokoki ta Ƙasa za ta iya, ta hanyar zartar da ƙudiri ta umarci Mataimakin Shugaban Ƙasa ya yi aikace-aikacen Ofishin Shugaban Ƙasa a matsayin Muƙaddashin Shugaban Ƙasa.
Kamar yadda Kundin Tsarin Mulki ya tanada, aikace-aikacen Mataimakin Shugaban Ƙasa sun haɗa da jagorantar dukkan tarukan tattaunawa na ministoci, da kuma kamar yadda doka ta tanada, zama memba na Majalisar Tsaro ta Ƙasa, Majalisar Zartarwa ta Ƙasa da kuma Shugaban Majalisar Tattalin Arziƙi ta Ƙasa.
Jaridar The Punch ta tattaro wasu manyan aikace-aikace waɗanda Mataimakin Shugaban Ƙasa, Osinbajo ba zai iya gudanarwa ba a lokacin da Buhari ba ya nan.
*Naɗe-naɗen muƙamai: Kamar yadda ake da Fadar Shugaban Ƙasa mai aiki a matsayin abu ɗaya, Mataimakin Shugaban Ƙasa ba zai iya yin wasu naɗe-naɗen muƙamai ba saboda Dokar da ta kafa mafi yawan hukumomin gwamnati da sashe-sashe ta bayyana ɓalo-ɓalo cewa ‘Shugaban Ƙasa zai naɗa’. Har Ma’aikata na Musamman na Mataimakin Shugaban Ƙasa Shugaban Ƙasa ne ke naɗa su, amma ana turo su ne ofushinsa kawai.
Tsohon Mataimakin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan ya bayyana haka a fili a shekara ta 2009 lokacin da ya ƙi ya rantsar da Alƙalin Alƙalan Najeriya, Mai Shari’a Aloysius Katsina-Alu, lokacin da Shugaba Umaru Musa Yar’adua ke Saudiyya don duba lafiyarsa. Alƙalin Alƙala mai barin gado na wancan lokaci, Mai Shari’a Idris Kutigi ne ya rantsar da wanda ya gaje shi.
*Sauke masu muƙamai: Za a iya tunawa cewa Osinbajo ne ya kori Muƙaddashin Darakta Janar na Hukumar Tsaro ta Farin Kaya, Lawal Daura a watan Agustan Bara yayinda Buhari ke hutu a Landan. Osinbajo ya iya yin haka ne saboda Muƙaddasin Shugaban Ƙasa ne shi a lokacin, saboda haka zai iya yin dukkan abinda Shugaban Ƙasa zai iya yi. Amma sakamakon ƙin miƙa masa mulki da Buhari ya yi a wannan lokaci, Osinbajo ba zai iya sauke wasu masu muƙamai ba, ko da an same su da ɗungushe. Dole ya jira shugabansa ya dawo. Haka kuma, Osinbajo ba zai iya yin garambawul ga majalisar zartarwa ko korar ministoci ba.
*Sa hannu ga dokoki: Ranar 12 ga watan Yuni, 2017, Muƙaddashin Shugaban Ƙasa, Osinbajo ya sanya wa Ƙudirin Kasafin Kuɗi na shekara ta 2017 hannu ya zama doka, kuma kasafin kuɗin ya fara aiki. Buhari, wanda ya kasance bisa hutun duba lafiyarsa na fiye da kwana 40 a wancan lokaci, ya miƙa iko ga Mataimakinsa ya yi aiki a madadinsa. A yanzu da Majalisar Dokoki ta amince da kasafin kuɗi, dole ‘yan Najeriya su jira Buhari ya dawo nan da mako mai zuwa kafin kasafin kuɗin ya zama doka.
*Ba dakarun soji umarni: Buhari, banda kasancewarsa Shugaban Ɓangaren Zartarwa na Gwamnati, shi ne kuma Babban Mai ba Dakarun Soji umarni. A taƙaice dai, Buhari shi ne kaɗai farar hular da sojoji suke karɓar umarni daga gare shi. Saboda wannan dalilin ne Jonathan ya kasa kiran Taron Tattaunawa na Jami’an Tsaro har sai da aka mayar da shi Muƙaddashin Shugaban Ƙasa ta hanyar amfani da Doctrine of Necessity a 2009. Duk da taɓarɓarewar yanayin tsaro a ƙasar nan, Osinbajo sai dai kawai ya kalla.
*Rubuta wasiƙa zuwa ga Majalisar Dokoki ta Ƙasa: Ba kamar a Amurka ba, inda Mataimakin Shugaban Ƙasa shi ne kuma Shugaban Majalisar Dattijai, Mataimakan Shugaban Ƙasa na Najeriya ba su taɓa yin wata mu’amala da Ofishin Shugaban Majalisar Dattijai ba, sai dai idan Mataimakin Shugaban Ƙasa yana aiki a matsayin Shugaban Ƙasa. Lokacin da yake Muƙaddashin Shugaban Ƙasa tsakanin 2016 da 2018, Osinbajo ya rubuta wa Majalisar Dattijai wasiƙa sau da yawa. Misali, a 2016, ya aika da wasiƙa ga Majalisar Dattijai, don ta tabbatar da Mai Shari’a Walter Onnoghen a matsayin Alƙalin Alƙalan Najeriya. Ya kuma aika da wasiƙa zuwa ga Majalisar Dattijai don ta tabbatar da Ibrahim Magu a matsayin Shugaban Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati, EFCC. Haka kuma, Osinbajo ba zai iya aikawa da ƙudurori zuwa ga Majalisar Dokokin ta Ƙasa ba.
*Bada sanarwar yaƙi ko kafa dokar ta ɓaci: Sashi na 305 na Kundin Tsarin Mulkin ƙasar nan ya bayyana ƙarara cewa Shugaban Ƙasa ne kaɗai zai iya kafa dokar ta ɓaci ko kuma bada sanarwar yaƙi.
Sashin ya ce: “Kamar yadda tanade-tanaden wannan Kundin Tsarin Mulki suke, Shugaban Ƙasa zai iya bada sanarwar kafa dokar ta ɓaci a faɗin tarayyar ƙasar nan ko wani ɓangare ta hanyar mujallar Gwamnatin Tarayya da aka buga.
“Shugaban Ƙasar zai yi gaggawa bayan buga sanarwar, ya miƙa kwafin mujallar Gwamnatin Tarayyar dake ƙunshe da sanarwar, da bayanin dokar ta ɓacin filla-filla, zuwa Shugaban Majalisar Dattijai da Kakakin Majalisar Wakilai, wanda su kuma kowane ɗayansu zai kira taron tattaunawa a Majalisar da yake Shugaban Majalisar Dattijai ko yake Kakaki, kamar yadda hali ya bayar, don su duba halin da ake ciki, sannan su yanke hukunci ko za su amince da dokar ta ɓacin ko kuma a’a”.