Wasu Yan Bindiga Sun Kai Hari Makarantar Mata A Zamfara

10

Wasu Yan Bindiga masu satar mutane sun kai hari a wata makarantan sakandare ta mata a jihar Zamfara inda suka yi awon gaba da mutanen da ba a tantance adadinsu ba.

BBC Hausa sun rawaito cewa Yan Bindigan sun kai harin ne a makarantar sakandare ta mata a garin Moriki da ke karamar Hukumar Zurmi da daddare a lokacin da ake kallon wasan zakarun Turai, kamar yadda wani mazaunin garin ya shaida musu.

Mutumin ya ce yan bingidar sun bude wuta a lokacin da suka shiga garin inda suka kashe wani mutum.

BBC Hausa sun kara da cewa wani dan Sa-Kai a garin na Morikei ya ce tun da la’asar yan bindigar suka tare haanya kafin daga baya suka kawo hari da daddare.

Mutumin ya kara da cewa sun tafi da wasu malamai biyu da wasu mata hudu, masu dafawa dalibai abinci amma ba su yi nasarar shiga inda dalibai ke bacci ba.
Mutane da dama ne dai suka rasa rayukansu, yayin da yara da dama suka zama marayu sakamakon kashe-kashen da ke faruwa a jihar.

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan