Yan Bindiga Sun Sace Surukin Dogarin Shugaban Kasa

169

A jiya laraba ne Yan bindiga suka kai hari garin Daura a jihar Katsina inda suka sace wani basarake daga garin haihuwa na shugaban kasa Buhari.

BBC Hausa sun tabbatar da labarin ta bakin shugaban karamar Hukumar Daura na riko, Injiniya Abba Mato wanda ya shaida cewa bayan sallar Magarba ne maharan suka kai farmaki a garin inda suka sace surukin dogarin Shugaba Buhari kuma magajin garin Daura, Alhaji Musa Umar.

Ya kara da cewa bayan shi da suka dauka, maharan ba su taba kowa ba, ba su harbi kowa ba sai suka tafi. Bayan samun wannan labari, jami’an tsaro sun dukufa wajen ganin sun kubutar da shi daga hannun yan bindiga.

Zuwa yanzu fadar shugaban kasa ba ta ce komai ba kan wannan lamarin. A jiya laraba, 1 ga watan Mayu aka yi jana’izar mutane 14 wanda suka rasa rayukansu sanadiyyar wani harin da aka kai karamar Hukumar Safana a jihar ta Katsina.

Honorable Abduljalal Haruna Runka, Dan Majalisar dokoki na yankin ya ce maharan sun kai farmaki a kauyen Gobirawa da kuma shaka Fito, kuma sun sace mata da wasu mutane.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan