Kotu ta soke zaɓen wani ɗan Majalisa a Adamawa

199

A ranar Juma’a ne Babban Kotun Tarayya dake Abuja ta soke zaɓen Abdulrauf Moddibo a matsayin sabon ɗan Majalisa da zai wakilci Mazaɓar Ɗan Majalisar Tarayya ta Yola ta Kudu/ Yola ta Arewa/ Girei ta Jihar Adamawa a Majalisar Dokoki ta Ƙasa.

Mai Shari’a Inyang Ekwo ya soke zaɓen Moddibo ne yayin da yake yanke hukunci a wata ƙara da Mustapha Mustapha ya shigar, inda yake ƙalubalantar zaɓen.

An bayyana Moddibo a matsayin wanda ya lashe zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar APC da aka gudanar ranar 7 ga watan Oktoba, 2018 a Yola, sakamakon haka ne ya wakilci jam’iyyar ta APC a babban zaɓen shekara ta 2019, wanda kuma aka ƙara bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara.

Usman ya maka Moddibo a kotu ne bayan zaɓen, yana zargin cewa ya yi ƙarya wajen bayyana shekarunsa, saboda haka bai kamata ya yi takarar zaɓen fitar da gwani na APC ɗin ba.

Ya roƙo kotun ta bayyana Moddibo a matsayin ɗan takarar APC na Mazaɓar Ɗan Majalisar Tarayya ta Yola ta Arewa/ Yola ta Kudu/ Girei da bai cancanta ba.

Usman ya lissafa jam’iyyar APC da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC a matsayin waɗanda yake ƙara a ƙarar.

A hukuncinsa, Mai Shari’a Ekwo ya bayyana cewa Modibbo bai cancanta ya yi takarar zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar APC da kuma zaɓen ‘yan Majalisar Wakilai na shekara ta 2019 ba.

Kotun ta tabbatar da cewa Usman ne halataccen wanda ya lashe zaɓen fitar da gwani na ranar 7 ga watan Oktoba, 2018, kuma shi ne halataccen ɗan takarar jami’yyar APC a mazaɓar.

Kotun ta ƙara tabbatar da cewa Usman ya yi nasarar kafa hujjar cewa Moddibo ya yi ƙaryar shekarunsa sau da dama don ya samu ya yi takara a zaɓen.

Kotun ta ce mai shigar da ƙara ya bada hujjar cewa lallai Moddibo ya miƙa takardun shaida na bogi don shiga takarar zaɓen fitar da gwanin.

Kotun ta ƙara tabbatar da cewa Moddibo yana aikin Hidimar Ƙasa a lokacin da ya yi takarar zaɓen fitar da gwanin, tana mai cewa hakan ya saɓa da Sashi na 4 na dokar da ta Kafa Hukumar Kula da Matasa Masu Yi wa Ƙasa Hidima, NYSC ta shekara ta 2004.

“Mutumin da yake mai karya doka ba zai iya zama mai yin doka ba; wannan rashin bin doka ba irin wanda za a gani a ƙyale ba ne”, in ji Mai Shari’a Ekwo.

Alƙalin ya ce duba da rashin cancanctar Moddibo, Usman wanda ya samu ƙuri’a ta biyu mafi yawa a zaɓen ranar 7 ga watan Oktoba, 2018 na jam’iyyar APC na Mazaɓar Ɗan Majalisar Tarayya ta Yola ta Arewa/ Yola ta Kudu/ Girei shi ne halataccen wanda ya lashe zaɓen.

Mai Shari’a Ekwo ya umarci jam’iyyar APC da INEC da su maye gurbin sunan Moddibo da na Usman a matsayin halattaccen ɗan takarar jam’iyyar APC a mazaɓar cikin gaggawa,

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan