Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Abubakar Sa’ad III ya tabbatar da ganin jinjirin watan Ramadan a Najeriya.
Sarkin, wanda shi ne Shugaban Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Ƙasa ya bayyana ganin watan a garuruwa da dama na Najeriya a wani taron manema labarai da aka yi ranar Lahadi da daddare.
A cewar Sarkin, wuraren da aka ga watan na Ramadan sun haɗa da Minna, babban birnin jihar Naija, Dutse, babban birnin jihar Jigawa da kuma Tsafe dake jihar Zamfara.
A cewar BBC, Kwamitin Ganin Wata na Najeriya ya wallafa jawabin Sarkin a shafin Twitter, inda Sarkin ya umarci jama’a da su tashi da azumi ranar Litinin.
Rahoton BBC ya ci gaba da cewa kasarin Musulmai a faɗin duniya za su tashi da Azumin watan Ramadan ranar shida ga watan Mayun 2019 wanda hakan ya zo dai-dai da ɗaya ga watan Ramadan 1440.
Sarkin ya yi kira da a yawaita ibada a cikin watan na Ramadan kuma a ci gaba da addu’a ga shugabanni.
Ramadan dai shi ne wata na 9 a cikin watannin Musulunci, kuma wata ne mai tarin alfarma, wanda Musulmai ke yawaita ibada a cikinsa don neman kusanci da Ubangiji.