Guardiola ya lashe kyautar gwarzon watan Aprilu

196
LONDON, ENGLAND - APRIL 14: manager Pep Guardiola of Manchester City reaction during the Premier League match between Crystal Palace and Manchester City at Selhurst Park on April 14, 2019 in London, United Kingdom. (Photo by Sebastian Frej/MB Media/Getty Images)

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City wato Pep Guardiola ya lashe kyautar gwarzon mai horas wa na watan Aprilu na gasar Premier ta kasar Ingila.

Ya lashe wannan kyautar ne bayan kungiyar kwallon kafan ta Manchester City ta lashe wasanni 5 a watan inda bata buga kunnen doki ba sannan kuma ba a sami nasara a kansu ba.

Manchester City dai a wasannin da suka buga guda 5 sun jefa kwallaye 9 inda aka jefa musu kwallo 1 kacal.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan