Majalisar Dokokin Jihar Kano ta gurgunta Masarautar Kano

162

A ranar Laraba ne Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da wata doka da za ta kafa ƙarin masarautu huɗu da sarakunan yanka guda huɗu a jihar.

Daily Nigerian ta gano cewa dokar da aka fara karatunta ranar Litinin, ta tsallake karatun farko ranar Talata, sannan ta tsallake karatu na biyu da na uku ranar Laraba.

“Babu wata hamayya a Majalisar. Waɗanda suke adawa da dokar sun fita”, in ji wani ɗan Majalisar da ya nemi a sakaye sunansa.

“Gwamna yana so ya rage tasirin Sarki Sanusi, saboda haka sai ya ƙirƙiri masarautun hamayyar ya kuma ɗora su a kan mataki ɗaya”

Sabuwar dokar, kamar yadda DAILY NIGERIAN ta yi tanadin cewa shugabancin Majalisar Sarakunan Jihar Kano zai riƙa zagayawa ne tsakanin Sarakunan.

Kamar yadda dokar ta tanada, sabbin masarautun da za a ƙirƙiro su ne Masarautar Kano, Masarautar Rano, Masarautar Gaya, Masarautar Ƙaraye da Masarautar Bichi.

Dama yau, Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yi alƙawarin sa wa dokar hannu da zarar an gabatar masa da ita.

Mista Ganduje ya bayyana haka ne ranar Laraba a wani taron manema labarai, kafin a fara Taron Tattaunawa na Majalisar Zartarwar Jihar Karo na 136 a Gidan Gwamnatin Jihar dake Kano.

“Mun ji wata doka da aka aika Majalisar Dokokin Jihar Kano dake roƙon su da su yi dokar da za ta ƙirƙiri sabbin Sarakuna a Kano.

“Mun yi imani cewa masu son a yi wannan doka sun yi haka ne da zuciya ɗaya. Kuma, suna son ci gaban jihar.

” Ina fata Majalisar Dokoki za ta yi aiki akan dokar, kuma ta gabatar min da ita don sa hannu, a shire nake in sa hannu ba tare da wani ɓata lokaci ba.

“Wannan shi ne abinda al’ummarmu suke so. Wannan kuma zai kawo ci gaba cikin gaggawa”, in ji Gwamnan.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan