Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi wa Shugabannin Majalisar gata

185

A ranar Talata ne Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da Dokar Haƙƙin Karɓar Fansho ta Kakakin Majalisa da Mataimakinsa ta 2019, wadda za ta ba shugabannin damar samun fansho har ƙarshen rayuwarsu.

Jaridar Daily Nigerian ta lura cewa banda fanshon na iya ƙarshen rayuwa, Kakakin Majalisar da Mataimakinsa za su damar tafiya waje don duba lafiyarsu, da sabbin motoci bayan kowace shekara huɗu.

“Za a riƙa biyan mutumin da ya riƙe muƙamin Kakakin Majalisa da Mataimakin Kakakin Majalisa fansho dai-dai da albashin Kakakin Majalisa da Mataimakin Kakakin Majalisa masu ci, matuƙar dai Kakakin ko Mataimakin Kakakin ba sa riƙe da wani muƙamin siyasa ko na naɗi”, in ji sabuwar dokar.

A cewar Dokar Fanshon, duk wani Kakaki da ‘yan Majalisun suka tsige shi ba zai amfana da fanshon da kuma sauran tagomashin da Dokar ta tanada ba.

“Duk wani mutum da aka zaɓe shi a matsayin Kakakin Majalisa ko Mataimakin Kakakin Majalisa, idan ya gama wa’adin mulkinsa, zai zama ya cancanci Jihar Kano ta riƙa ba shi fansho har iya rayuwarsa, matukar dai ba ‘yan Majalisar Dokokin Jihar Kano ne suka kawar da wannan mutumin daga ofis ta hanyar tsigewa ba.

“Za a riƙa biyan Kakakin Majalisa ko Mataimakin Kakakin Majalisa a ƙarshen wa’adin mai riƙe da muƙamin.

“Inda Kakakin Majalisa ko Mataimaki ya bar ofis kafin ƙarewar wa’adin mulkinsa, ba a sakamakon tsigewa ba, za a biya shi fansho na adadin shekarun da ya yi a wa’adin mulkin.

“Inda kuma Kakakin Majalisa ko Mataimakin Kakakin Majalisa ya mutu a kan mulki kafin wa’adin mulkinsa ya cika, za a biya shi fansho na adadin shekarun da ya yi a wa’adin mulkin

“Za a riƙa samar wa Kakakin Majalisa da Mataimakin Kakakin Majalisa sabuwar mota, wadda Gwamnatin Jihar za ta riƙa siyowa duk bayan shekara huɗu”, a cewar sabuwar dokar.

“Za a riƙa samar wa da Kakakin Majalisa da Mataimakin Kakakin Majalisa damar duba lafiya a gida ko a waje, ya danganta da yanayin cutar”

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan