Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Tottenham kuma dan asalin kasar Brazil wato Lucas Moura ya kafa tarihi a wasan da Tottenham Hotspur ta buga a daren jiya da kungiyar kwallon kafa ta Ajax.
Tarihin daya kafa shine tunda aka fara gasar zakarun nahiyar turai ba a taba samun wani dan wasa daga kasar Brazil daya taba cin kwallaye guda 3 ba a wasan kusa dana karshe sai shi.

Anyi manyan ‘yan wasan da sukayi sharafi a kasar Brazil kuma suka nuna kansu a tarihin gasar zakarun turai irin su Kaka da Ronaldo da Roberto Carlos da Ronaldinho da Rivaldo da Neymar da sauransu amma basuyi irin abin da Moura yayi ba.
Turawa Abokai