A ƙalla wasu manyan ‘ya’yan Sarki sun yi watsi da tayin muƙamin da aka yi musu na Sarkin Bichi, ɗaya daga cikin masarautu huɗu da Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ƙirƙira ranar 8 ga watan Mayu.
DAILY NIGERIAN ta samu tabbacin cewa Gwamnan ya gana da Wamban Kano, Aminu Bayero, Ciroman Kano, Nasiru Bayero da hakiman Rano, Gaya da Ƙaraye a Gidan Gwamnatin Jihar Kano ranar Alhamis da daddare.
Majiyoyin cikin gida sun ce Ciroman Kano aka fara yi wa tayin muƙamin Sarkin Bichi, inda nan take ya yi watsi da ita.
Daga nan sai Gwamnan ya miƙa tayin ga yayan Ciroma, Aminu Bayero, wanda ya ce yana buƙatar lokaci don ya yi shawara.
Majiyoyin dake kusa da shi sun shaida wa DAILY NIGERIAN cewa shi ma daga bisani ya yi watsi da tayin.
Zaɓin Mista Ganduje na uku shi ne Galadiman Kano, Abbas Sanusi, mahaifin Abdullahi Abbas, Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano.
“Lokacin da aka yi wa Galadima tayin, sai ya tuntuɓi Sarki Sanusi, yana sanar da shi game da matakin. Sarkin ya faɗa masa cewa a halin yanzu zaɓi ya rage ga Zuri’ar Gidan Dabo su zama an haɗa baki da su an kashe abinda suka gada, ko kuma su zama masu kare abinda suka gada”, wata majiya a Fadar Sarkin ta jiyo shi yana faɗar haka.
“Daga dukkan alamu, babu alamar Galadima zai karɓi tayin. Shi ma yana fushi da ƙirƙiro ƙarin masarautu a Kano”, in ji majiyar.
DAILY NIGERIAN ta gano cewa bayan ‘ya’yan Sarkin sun yi watsi da tayin, sai Gwamna Ganduje ya bar muƙamin Sarkin Bichi ba kowa, ya kuma ɗaga darajar hakiman Rano, Gaya da Ƙaraye zuwa muƙamin Sarki a yayin taron tattaunawar.
Wasu majiyoyi sun ce ranar Juma’a da safe Gwamna Ganduje ya bar Kano zuwa Abuja don ganawa da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo bisa abubuwan dake faruwa a jihar Kano.