Laifukan Sarkin Kano Sanusi 3

353

Na farko, matsanancin son mulki. Tun kafin ya zama sarki, ya yi ta bayyana wa duniya kulafucinsa ga sarautar Kano. Wannan tsananin so a kashin kansa dama ce ga makiyi na ya cutar musamman a inda aka samu Sarki da tawaya.

Na biyu, rashin rike kai. An samu Sarki da zargin almubazzaranci, jaridar Daily Nigerian ta ba da rahoto a kai. Kazalika an samu Sarki da yawan sa baki a kan lamurran da suka shafi ‘yan siyasa alhali ya zabi zama bagargajiye uban kowa. Ministan Ilimi na yanzu, Malam Adamu Adamu, ya taba jan kunnensa a lokacin da yake rubutu a shafin Daily Trust kan yawan surutu. Ya bukaci ya sa wa bakinsa amawali. Amma bai ji ba.

Na uku, Sarki ya ware wani bangare na al’ummarsa da hantara. Kusan a kowace gaba ya samu dama sai ya nuna nukurarsa gare su. A matsayinsa na Sarki uban kowa, ya kamata ya zamana, Musulmi da dukkan rabe-rabensu, Kiristoci da dukkan farrake-farrakensu, Maguzawan gargajiya da hatta Mulhidan zamani, a ce, dukkansu za su iya samun wurin rabewa a zuciyarsa. Saboda haka sarautar ta gada kuma ta gadar.

Haka Marigayi Ado Bayero ya kasance. Amma Sarki ya ki kallon haka, ya sa mabiya Ahlulbaiti (as) a gaba da hantara da suka duk kuwa da cewa ba su yi masa laifin komai ba. Wannan ya sa Farfesan Tarihi, Dahiru Yahya, ya tunatar da Sarkin cewa a cikin Sarakunan Kano na baya akwai wanda ya bi tafarkin Shi’a. Abin mamaki, Sarkin ya kasa musawa da hujja karbabbiya.

Ababen Dubawa

Ga Sarki mai tsananin son mulki, bai kamata a same shi da almubazzaranci ba. Saboda makiyansa za su iya amfana da haka wurin bakanta shi. Idan kuma har aka same shi da hakan, to, bai kamata ya ba wa kansa aikin sukar motsin ‘yan siyasa ba. Saboda za su hana sarautarsa zaman lafiya.

Idan kuma duk da hakan ya ce dole sai ya tsoma baki a harkokin ‘yan siyasan, to, bai kamata ya rika nuna hantara ga wani bangare na al’ummar kasarsa ba. Saboda zai bukace su a lokacin da ‘yan siyasar nan suka nemi hana sarautarsa zaman lafiya.

A matsayin Sarki Sanusi na mufakkirin mai ilimi, na yi mamaki da ya ki kallon wadannan ababe. Ina fikira da hazakarsa suka tafi?

Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi II

Adalcin da ya sa ake nuna rashin dacewar abin da Gwamna Ganduje ya yi masa, irin wannan adalcin ke tilasta shi ma a kalli nasa janibin. Sarki Sanusi yana bukatar taka wa kansa birki a wasu wurare tunda jimawa.

A ranar da aka ce an nada Muhammadu Sanusi Sarkin Kano, na yi takaicin rashin mufakkiri ga al’ummar Arewa. Domin ya jefa kansa inda ba za a bari fikira da himmarsa su yi aiki ba. Na san shi a rubutu ba a fuska ba, tun yana bankin UBA a Kano. Kuma tun daga lokacin nake karanta duk abin da ya rubuta.

A sarauta, babu abin da zai kara ko ya rage na fadakarwa da ayyukan kasa. Idan ya ce zai fadakar ne, to, ‘yan siyasa da masu mulki ba za su natsu da shi ba. Idan kuma ya ce aikin bunkasa rayuwar jama’a zai yi, shi ma ba zai iya ba saboda akwai wadanda aka tanada musamman don yin haka.

To mene ne amfanin sarautar ga hazikin mufakkiri irinsa?

Tambayar ke nan da na yi wa wata da ke cikin gidan sarautar. Sai ta ce, haka ‘ya’yan sarakuna suke.

Na rasa yadda za a yi wannan amsa ta kama hankalina, yayin da na tuna da rayuwar Marigayi Dr Bala Usman na Jami’ar ABU. Dan sarautar Katsina ta wurin uba, kazalika dan sarautar Kano ta wurin uwa. Amma duk da haka ya zabi ya karar da rayuwarsa a jami’a inda fikirarsa za ta sakata ta wala.

Sarki Sanusi ya fi Dr Bala Usman faffadan fikira a ra’ayina. Saboda yana da ilimin Musulunci. Sai dai kuma abin takaici, ya jefa kansa inda ba zai samu damar amfanar da kowa fikirarsa kamar Dr Bala Usman ba. A karshe ma, ya ja wa kansa wulakanci daga wadanda suka dauki aikin kaskanci ba laifi ba. Wannan lamari yana sa ni tuna wata ruwaya mai cewa: “Babu abin da ya fi muni ga Mumini a kan kwadayin da ke kaskanta shi.”

Daga Muhammad Bin Ibrahim

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan