Na Yi Wa Sarki Sanusi Nisa, Shugaban Ƙaramar Hukuma Ne Dai-Dai Da Shi Ganduje

199

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa shi ba sa’an Sarkin Kano Muhammadu Sanusi bane ko a tsarin dokar ƙasa. Ganduje ya ce da shugaban karamar hukuma ya kamata yana sa-in-sa ba gwamna ba domin nan ne hurumin sa sannan daidai shi.


“Gyara ne da ci gaba muka kawo jihar mu. Muna so mu kusanto da mutane kusa da shugabannin su. Amma ba daukar fansa ba ko kuma bibiyar wani”
“Idan ma har zancen ake so a yi ai a ƙarƙashin shugaban karamar hukuma ya ke ba gwamna ba.


” Idan ba domin wasu dalilai ba, ai da shugaban karamar hukuma ya kamata yake gani idan bukatar haka ta tashi ba gwamna ba, domin gwamna ya yi masa nisa. Haka dokar kasa ta gindaya.


A ƙarshe Gwamnan ya bayyana cewa wannan masarautu da muka kirkiro za mu tabbata mun gyara su sannan mun daga darajarsu da martaba a idanun mutanen jihar, domin kuwa mutanen jihar Kano suna murna da wannan mataki da gwamnati ta ɗauka.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan