Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu, JAMB ta ce za ta saki sakamakon Jarrabawar Bai Ɗaya ta Shiga Manyan Makarantu, UTME ta 2019 ranar Asabar.
Magatakardar Hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede ya bayyana haka ga manema labarai ranar Juma’a a Abuja.
“Gobe (yau) za mu saki sakamakonmu. Za mu tattauna yau (jiya) don mu duba me za mu fitar”, in ji Farfesa Oloyede.
An gudanar da jarrabawar UTME ne daga 11 zuwa 18 ga watan Afrilu, kuma fiye da ɗalibai miliyan 1.8 suka yi rijista.
Tun lokacin, har yanzu Hukumar ba ta iya sakin sakamakon jarrabawar ta UTME ba.
Ta bayyana cewa da farko sai ta fara tantance sakamakon ɗaliban gaba ɗaya don gano waɗanda suka yi maguɗi yayinda ake gudanar da jarrabawar.
Haka kuma, Magatakardar ya yi holin wani ma’aikacin Hukumar wanda ake zargin ya karɓi N25,000 daga wani ɗalibi da ya nemi gurbin karatu a shekara ta 2018.
Ya ce an kawo ƙarar wanda ake zargin ne zuwa Hukumar Gudanarwar JAMB bayan ya kasa biya wa ɗalibin buƙatarsa.
Magatakardar ya ce Hukumar a shirye take wajen sa ƙafar wando ɗaya da duk wanda aka samu yana cin amana, ko ma’aikacinta ne.
“Ba ma ɓoye komai; a shirye muke mu hukunta duk wanda aka kama, kuma dole su fuskanci fushin hukuma”, in ji shi.