Ƙirƙirar Masarautu: Al’ummar Wudil sun ɓalle

184

Biyo bayan ƙirƙirar sabbin masarautu huɗu a jihar Kano, ƙungiyoyin al’umma da dama a Wudil sun bayyana cewa su fa za su ci gaba da yi wa Masarar Kano ne mubaya’a ba Masarautar Gaya ba kamar yadda sabuwar dokar ƙirƙirar sabbin masarautun ta nuna.

Da yake yi wa manema labarai jawabi jim kaɗan bayan wani taron taron tattaunawa na haɗin gwiwa na masu ruwa da tsaki daga ƙaramar hukumar Wudil ƙarƙashin jagorancin Malam Yawale Muhammad Idris, Sakataren Ƙungiyar Haɗin Gwiwar Masu Ruwa da Tsaki ta Wudil, Dakta Baffa Sani Wudil ya ce an ƙirƙiro sabbin masarautun ne ba tare da tuntuɓar al’ummar Wudil ba, kuma yunƙurin ya ci karo da tsohon tarihin da yankin ke da shi.

“Mu ba mu nemi haka ba kwata-kwata, kuma lokacin da gwamnati ta yanke shawarar ƙirƙirar sabbin masarautun, ba a tuntuɓi al’ummar Wudil ba. Saboda haka, muna da tabbas cewa idan aka ƙyale wannan doka ta ci gaba da zama babu shakka za ta goge tushen tarihinmu, kuma al’ummar Wudil ba za su bari haka ta faru ba.

“Mun yi amanna cewa masarauta tana da dogon tarihi, kuma hakan shi yake nuna su wane mu. Mu ne Joɓawa, kuma muna so Gwamna Ganduje ya san haka.

“Kuma za mu bayyana a nan cewa, dukkan masu ruwa da tsaki a Wudil za su yi mubaya’a ne ga Kano ba Masarautar Gaya ba”, in ji shi.

Ya kuma ƙara bayyana cewa al’ummar Wudil za su gabatar da kokensu a wajen dukkan hukumomin da suka dace don neman mafita.

A cewarsa, Ƙungiyar Masu Ruwa da Tsakin za ta yi amfani da dukkan matakan Shari’a na ƙasar nan don ganin cewa Wudil ta ci gaba da kasancewa a Kano, ba Gaya ba kamar yadda sabuwar dokar ƙirƙirar masarautun ta nuna.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan