EFCC ta ƙwace gidajen Saraki

61

Hukumar Hukunta Masu Yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati, EFCC ta ƙwace wasu gidaje mallakin Shugaban Majalisar Dattijai, Dakta Abubakar Bukola Saraki, a cewar rahoton jaridar SUNDAY PUNCH

Rahotanni sun ce gidajen suna 15a, 15b, da 17 akan Titin MacDonald, Ikoyi, Legas.

Amma, jaridar dake da karɓuwa sosai a ƙasar nan ta ce EFCC ba ta da tabbacin wane ne daga cikin gidajen yake mallakin Saraki, sakamakon haka ne ta sa alamar rubutu da sitika a kansu gaba ɗaya.

Yayinda da rahotanni suka ce Saraki ya bayyana gida mai lamba 15a da 15b a fom ɗin bayyana kadarorinsa, SUNDAY PUNCH ta ce an yi amanna cewa Shugaban Majalisar Dattijan ya sayi wasu gidaje dake kan titin daga a daga Kwamitin Aiwatar da Siyar da Kadarorin Gwamnati ta hannun kamfanonin shell.

Wasu daga cikin gidajen suna daga cikin waɗanda aka yi ƙarar Saraki a kansu a gaban Kotun Ɗa’ar Ma’aikata, CCT, wadda daga bisani ta yi watsi da ƙarar sakamakon rashin hujja.

Amma EFCC ta ƙara ci gaba da binciken Saraki bayan ƙarar kotun.

A makon da ya gabata EFCCn ta rubuta wasiƙa zuwa Gwamnatin Jihar Kwara, inda take buƙatar a ba ta bayanin yadda jihar ta kashe kuɗaɗenta a shekaru takwas da Saraki ya yi a matsayin Gwamna.

Saraki ya zama Gwamnan Jihar Kwara daga 2003 zuwa 2011, lokacin da ya tafi Majalisar Dattijai.

Ya kasance Shugaban Majalisar Dattijai daga 2015 zuwa yanzu,, inda yunƙurin tsige da aka yi da dama duk ba su yi nasara ba.

Amma Saraki ya yi watsi da wannan sabon bincike da EFCC ke yi masa, yana mai bayyana shi da cewa bi ta da ƙulli ne.

A wata sanarwa da ya fitar makon da ya gabata ta bakin Mai Ba Shi Shawara na Musamman Kan Kafafen Watsa Labarai, Yusuph Olaniyonu, Saraki ya ce kamar yadda yunƙurin baya na tumɓuke shi bai yi nasara ba, na baya-bayan nan ma ba zai yi nasara ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan