Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta zamo zakara a gasar ajin Premier ta kasar Ingila kakar wasa ta 2018 zuwa ta 2019.
City sun zamo zakara ne bayan sun doke Brighton And Hove Albion da ci 4 da 1 a wasan karshe da suka buga na gasar a yammacin yau Lahadi.

Inda suka yi takarar lashe wannan kofi da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool inda sukuma Liverpool suka lallasa Wolves daci 2 da nema.
Yanzu dai ta tabbata cewa City sun lashe kofin da maki 98 kuma karo na 2 a jere a karkashin jagorancin mai horas wa Pep Guardiola.
Wannan ne karo na farko da aka samu kungiyoyin kwallon kafa guda biyu a tarihi da suka hada maki 90 da doriya ba a sami Kungiyar data lashe kofin ba sai a wasan karshe.

Ga cikakken sakamakon wasannin na yau.
Brighton & Hov… 1 – 4 Manchester City
Burnley 1 – 3 Arsenal
Crystal Palace 5 – 3 AFC Bournemouth
Fulham 0 – 4 Newcastle United
Leicester City 0 – 0 Chelsea
Liverpool 2 – 0 Wolverhampton
Manchester United 0 – 2 Cardiff City
Southampton 1 – 1 Huddersfield Town
Tottenham Hotspur 2 – 2 Everton
Watford 1 – 4 West Ham United
Kuma rabon da a sami wata kungiyar kwallon kafa data lashe gasar sau 2 a jere tun 2009.
a yanzu dai kungiyoyin kwallon kafan da suka sami tikitin buga gasar zakarun turai sune:
- Manchester City da maki 98.
- Liverpool da maki 97.
- Chelsea da maki 72.
- Tottenham da naki 71.

Kungiyoyin kwallon kafan da suka samu koma baya sune:
Cardiff City.
Fulham.
Huddersfield Town.
Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Aubameyang shine ya lashe takalmin zinare na gasar da kwallaye 22.