Ganduje ya ba Sarki Sanusi zaɓi uku

244

Ƙirƙirar sabbin masarautu da aka yi ranar Laraba a jihar Kano ba lallai ya zama ƙalubale na ƙarshe da Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II zai gani ba, domin kuwa binciken Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafen Jama’a da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano ke yi wa Sarkin ka iya haifar da a tattara laifuka har a maka shi a kotu, kamar yadda jaridar Sunday Trust ta gano.

An dakushe matsayin Sanusi ne a matsayin Sarkin Yanka Ɗaya na Jihar Kano lokacin da Gwamnatin Jihar ta raba masarautar, ta samar da sabbin masarautu huɗu, ta kuma naɗa sarakunan yanka don su mulke su.

Dokar ƙirƙirar masarautun, wadda ta ɗauki kwana biyu kaɗai, ta jawo ce-ce-ku-ce cewa Gwamnatin tana neman cire Sarkin ne bisa goyon bayan da ake zargin ya ba ba jam’iyyar PDP a zaɓen gwamna da aka yi kwanakin baya.

Sabon binciken da Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafen Jama’a da Yaƙi da Cin Hanci Ta Jihar Kano ke yi da ƙirƙirar sabbin masarautu da Majalisar Dokokin Jihar ta yi kusan lokaci ɗaya suka faru a makon da ya gabata.

A jiya ne wata majiya da ta nemi a sakaye sunanta ta shaida wa wakilin jaridar cewa binciken da Hukumar ke gudanarwa a halin yanzu Sarkin ake so a cimma, tana mai lura da cewa: “Za a kai wata gaɓa da Hukumar za ta kai abin kotu, don Sarkin ya kare kansa. Bayan bincikenmu, duk mutumin da aka samu da laifin ɓanna da kuɗin al’umma za a maka shi a kotu”.

A jiya ne wata majiyar gwamnati ta bayyana cewa bayan da Sarki Sanusi ya hango matsala game da yadda abubuwa ke gudana kwanan nan tsakanin gwamnati da Fadar, sai ya tura babban ɗan kasuwa, Aliko Dangote don ya roƙi Gwamna Ganduje ya sake tunani.

“Zan iya faɗa maka da ƙarfin guiwa cewa lokacin da aka sabunta binciken, kuma aka fara yunƙurin ƙirƙiro sabbin masarautu a jihar nan, sai Sarkin ya tura shahararren ɗan kasuwar nan, Aliko Dangote wajen Ganduje don ya roƙe shi ya dakatar da yunƙurin guda biyu.

“Amma, Ganduje a amsarsa, sai ya faɗa wa Dangote ya koma ya faɗa wa Sarki ya zaɓa daga cikin zaɓi uku: Ko ya ajiye mulki da kansa, ko a sauke shi, ko kuma gwamnati za ta ƙirkiri sabbin masarautu a jihar.

“Ganduje ya tabbatar wa Dangote cewa dole gwamnati za ta aiwatar da ɗaya da ɗaya daga cikin zaɓin guda uku, tunda Sarkin ba zai daina yaƙar Gwamnan ba a siyasance. Ba don tsoma baki da Dangote ya yi cikin gaggawa ba, da tuni Ganduje ya sauke Sarkin”, in ji majiyar.

“Amma, majiyar ta ƙara da cewa koda yake Gwamnan ya ajiye maganar sauke Sarkin, akwai yiwuwar bayan an gama bikin naɗin sabbin sarakunan, Ganduje zai tura Sarkin zuwa wata masarautar, ya maye gurbinsa da ɗaya daga cikin sabbin sarakunan da aka naɗa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan