Hanyoyi Bakwai Da Azumi Ke Kara Lafiya Ga Jikin Dan Adam

347

A yayin da musulmi a fadin duniya ke share wata guda ba tare da ci ko sha ba daga fitowar Alfijir zuwa faduwar rana a watan Ramadan, Masana sun gano cewa yin hakan yana da tasiri matuka ga lafiyar jikin Dan Adam.

Bincike ya nuna cewa Azumin yana taimakawa yanayin jikin Dan Adam, ta hanyar bunkasa aiyukansa. Ga hanyoyi Bakwai da Azumi ke kara jikin Dan Adam Lafiya

  1. Bude Baki Da Dabino: Ya zo a hadisin Manzon Allah SAW cewa ana so duk mai azumi ya yi bude baki da dabino idan akwai wadatar hakan. Masana a fannin lafiya sun gano cewa yin bude baki da dabino guda uku ga mai azumi yana taimaka wa wajen samar da sinadirai masu bawa Dan Adam kuzari a jiki kamar su Carbohydrates, da Potassium, da Magnesium da Vitamin B da sauransu. Hakan yana taimaka wa lafiyar mutum ta hanyoyi da dama.
  2. Bunkasa Kwakwalwa: Azumi yana bunkasa aikin kwakwalwar Dan Adam. Wani bincike da aka gudanar a kasar Amurka ya gano cewa a lokacin Azumi kwakwalwa tana samun raguwar aiyukanta kuma hakan na bata damar kirkirar sabbin kwayoyin hallitar ta wanda don bunkasa aiyukanta. Hakan na kara kaifin kwakwalwar mutum da aikin ta.
  3. Bin Ka’idar Cin Abinci: Mafi yawan cin mutane a lokacin da suke Azumi suna yin bude baki ne da kayan abinci masu gina jiki da kara lafiya. Hakan yana matukar tasiri ga jikin wajen inganta lafiya da bunkasa aiyukansa. Jama’a da dama suna daina shan taba sigari, da suna rage ciye-ciyen kayan zaki da dai sauransu. Azumi yana ba jikin Dan Adam damar samun abinci masu kara lafiya da sa kuzari sannan ya yi aiki cikin yanayi mai kyau.
  4. Rage Kiba: Sanan nen abu ne ga kowa cewa a watan Ramadan jama’a na rage kiba saboda azumin da ake yi. Hakan yana taimaka wa lafiya jikin Dan Adam ta hanyar rage yawan maikon da ke cikin jikin. Idan maikon Cholesterol na jikin mutum ya ragu, ana sa ran ya fita daga fadawa cikin hadarin kamuwa da ciwon zuciya da sauran cututtuka da yawan maiko a jiki ke haifarwa.
  5. Cin Abinci Mai Inganci: Azumi yana samar da yanayi na cin abinci mai inganci wanda Idan mun lura, zamu ga jama’a da dama suna hada kusan dukkanin rukunin abinci mai inganci (balance diet) a lokacin buda baki. Wannan ya kan zama wata dama da jiki ke samun kusan dukkanin rukunin abinci masu inganci da ya ke bukata domin gudanar da aiyukansa. Don haka azumi yana ba jiki Dan Adam damar samun nau’o’in abinci masu inganci da yake bukata don yin aiki yadda ya kamata.
  6. Tsarkake Jiki: Azumi wata dama ce da jikin Dan Adam ke samu ya tsarkake kansa watau Detoxification. A yayin da mutum ya ke azumi, Jikinsa yana kokarin amfani da kwayoyin hallita da ke ajiye, kuma yana kawar da duk wani abinci ko sha da ya shiga jikin marar amfani. Kusan wani yanayi ne da jiki ke tsaftace kansa da kansa domin inganta lafiya. Don haka azumi yana ba jikin Dan Adam damar cire nau’ikan abinci marasa amfani ga jikin.
  7. Karin Kuzari Ga daukacin Jiki: A yayin da mutum ya ke Sahur da Asuba, sannan ya yi bude baki da magariba, hakan na samar da wani yanayi mai inganci ga jiki. Jikin Dan Adam na kara yawan fitar wani kwayan halitta mai suna Adiponectin Hormone wanda ya ke taimaka wa sassan jiki su yi amfani da kwayoyin masu inganci na abinci a cikin jikin. Anan, shi kanshi jikin yana samun karin kaimi wajen ta ce abincin da zaben nau’ikan abinci masu inganci domin amfanin bangarori dabam-dabam.

Don haka, jiki baki daya yana samun lafiya, da karin kuzari da inganci a lokacin azumin watan Ramadan.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan