INEC ta ƙwace Takardar Shaidar Cin Zaɓe da ta ba wani sanata

179

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC ta janye Takardar Shaidar Cin Zaɓe da ta ba Peter Nwaoboshi.

Hukumar Zaɓen ta ba Ned Nwoko Takardar Shaidar Cin Zaɓen biyo bayan wani umarnin kotu da ya tabbatar da Mista Nwoko a matsayin sahihin ɗan takarar jam’iyyar PDP na Mazaɓar Sanata ta Delta ta Kudu a zaɓen 23 ga watan Fabrairu.

Mista Nwoko ya karɓi Takardar Shaidar Cin Zaɓen ne ranar Juma’a, kuma jaridar PREMIUM TIMES ta ga kwafin shaidar ta Intanet ranar Lahadi da yamma.

Wannan mataki na INEC ya zo ne wata ɗaya bayan Babbar Kotun Tarayya ta yanke hukuncin cewa an cuci Mista Nwoko ne lokacin da aka yi zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar PDP a Mazaɓar Sanatan.

Ahmed Muhammed, ya tabbatar da cewa Mista Nwoko ya samu kuri’a 453, inda ya kayar da Mista Nwaoboshi, wanda ya samu kuri’a 405.

Mista Nwaoboshi, wanda aka fara zaɓen sa zuwa Majalisar Dattijai a shekara ta 2015, ya ɗaukaka ƙara cikin gaggawa.

Amma sai Hukumar Zaɓen ta yanke shawarar yin amfani da hukuncin Babbar Kotun Tarayya, ta tabbatar da Mista Nwoko a matsayin zaɓaɓɓen sanata.

Mista Nwoko, ɗan shekara 59, ya taɓa zama mamba a Majalisar Wakilai ta Ƙasa daga 1999 zuwa 2003.

Kwanan nan ne kuma ya yi suna a kafafen Sada Zumunta lokacin da ya sanar da aurensa ga ‘yar fim ɗin Nollywood, Regina Daniels.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan