Abubuwan Da Mai Azumi Ya Kamata Ya Yi, Don Rage Kishin Ruwa

214

A wannan yanayi na matsanancin zafin rana da ake gudanar da Azumin watan Ramadana, mutane da dama kan tsinci kansu cikin mawuyacin hali saboda rashin samun damar shan ruwa.
Hakan ya kansa wasu su kasa sukuni, wasu ma har sukan fita hayyacinsu, su suma. Don haka, yana da kyau mai azumi ya san abubuwan da ya dace ya yi don gujewa fadawa cikin mawuyacin hali.
Masana lafiyar jikin Dan Adam sun bada shawarwarin abubuwan da mai azumi ya kamata ya yi kamar haka:

  1. Yana da kyau mai azumi ya guji shan ababen sha da ya ke dauke da Caffaine. Caffaine wani sinadari ne da idan ya shiga jikin Dan Adam, yana fitar da ruwa da gishiri ta hanyar sanya yawan fitsari. Idan mai azumi ya sha Caffaine, zai sa shi yawan jin kishi saboda yawan fitsari da zai ta yi.
  2. Sannan Ana so mai Azumi ya yi buda baki da kayan marmari da ganyayyaki. Buda baki da kayan marmari da ganyayyaki yana taimaka wa jiki wajen rike ruwa a cikin jiki a yayin da mutum ya ke cigaba da Azumi.
  3. Mai Azumi ya guji cin abinci da aka sa gishiri da yawa ko kuma yaji. Duk abinci mai dauke da wadannan abubuwa biyu da yawa kan sa jikin Dan Adam ya kasa rike ruwa wanda hakan zai janyo kishi ga mai Azumi.
  4. Yana da matukar amfani ga lafiyar jikin Dan Adam ga mai Azumi ya guji shiga rana ko da kuwa aikin mutum yana bukatar hakan. Idan mai Azumi ya shiga rana, to ya san yadda zai yi ya samar da Inuwa a kan sa. Yawan shiga cikin rana ba tare da samun kariya ba, yana haifar da rashin ruwa a jikin Dan Adam. Hakan zai iya janyo kasala ko mutuwan jiki ko ya sa mutum ya suma idan abin ya yi tsanani.
  5. Mai Azumi ya guji shan ruwaa ko wani abun sha dayawa idan anyi buda baki. Hakan yana ba wa yanayin jikin Dan Adam Matsala musamman idan abin shan yana da sanyi sosai. Ya fi dacewa mutum ya sha kadan-kadan har lokacin da jikin zai dai-daita.
  6. Idan gari ya yi zafi sosai, to yana da kyau mai Azumi ya watsa ruwa a jikinsa saboda samun saukin zafi gari da rashin shan ruwa. A wannan lokaci na yanayin zafi, idan ruwan jikin mutum ya yi karanci, ana iya ganewa ta hanyar yawan gajiya, da bushewar baki, da kishi, da ciwon kai. Don haka mai Azumi zai iya rage kishi ta hanyar zuba ruwa a jiki
Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan