Home / Cigaban Al'umma / Gwamna Shettima ya yi nasara a kotu

Gwamna Shettima ya yi nasara a kotu

Ranar Talata ne Kotun Sauraron Ƙorafe-ƙorafen Zaɓe ta Jihar Borno dake zamanta a Abuja ta yi watsi da ƙarar da Sanata Mohammed Abba Aji na jam’iyyar PDP ya shigar gabanta, inda yake ƙalubalantar nasarar da Gwama Kashim Shettima na jam’iyyar APC ya samu a matsayin wanda ya lashe zaɓe a Mazaɓar Sanata ta Borno ta Kudu.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya bada rahoton cewa Abba Aji ya wakilci Mazaɓar daga shekarar 2003 zuwa 2007.

A wata ƙara mai lamba EPT/BO/SEN/3/2019, da kwanan watan 17 ga watan Maris da aka shigar a gaban Kotun dake zama Abuja: “Abba ya ce akwai aringizon ƙuri’u a mazaɓu bakwai, da hujjar abubuwan cin hanci, da kuma rashin bin Dokar Zaɓe”.

Waɗanda Mista Abba Aji yake ƙara su ne jam’iyyar APC da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC.

Da yake yanke hukunci, Alƙalin Kotun, Mai Shari’a Peter Kekemeke, ya ce kotun ta yi watsi da ƙarar ne sakamakon rashin cancancta.

“Masu shigar da ƙarar ba su yi amfani da tanadin da Sashi na 49 na Farkon Dokar Zaɓe ya yi ba”, in ji Mai Shari’a Kekemeke.

About Hassan Hamza

Check Also

Wasiyyar da marigayi tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’adua ya barwa ƴan siyasar Najeriya

A yau Laraba 5 ga watan Mayun shekarar 2021 tsohon shugaban Najeriya Malam Umaru Musa …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *