Hukumar UNICEF Ta Baiwa Jihar Kogi Agaji A Fannin Ilimi

161


Hukumar UNICEF ta taimaka wa gwamnatin jihar Kogi ta bangaren fasaha domin shirya dabaru masu inganci a sashin ilimin jihar.

Mai bada shawara ga hukumar, Misis Seyi Agunbiade ce ta bayyana wa manema labarai hakan, bayan kammala ganawa da ta yi da kwamishinar Ilimi, da Kimiyya da Fasaha a jiya Litinin, 13 ga watan Mayu a garin Lokoja.

Misis Seyi ta ce da irin wannan tsari, gwamnati zata iya amfani da shi wajen fitar da kudi domin bunkasa fannin ilimi a jihar kuma hakan zai ba wa masu bada agaji daga kasashen waje daman yin taimako ga jihar.
Ta kara da cewa, idan har akwai kyakkyawan tsari akan fannin Ilimi, hakan zai sa gwamnatin jihar Kogi ta cimma burin ta na samar da ilimi.

Daga nan ta yaba wa kwamishinar Ilimi ta jihar bisa kokarin ta na tabbatar da tsari mai kyau na Ilimi a jihar wanda yana daga cikin hanyoyin cigaba ga jihar.

A nata bangaren, kwamishinar Ilimi, da Kimiyya da Fasaha, Misis Rosemary Osikoya ta mika godiyar ta ga hukumar UNICEF bisa yadda ta ke taimaka da kuma gudunmawatta ga fannin Ilimi a jihar.

Misis Rosemary ta ce kwalliya na biyan kudin sabulu bisa kokarin da su ke yi don inganta Ilimi a jihar. Ta ce wannan kadan ne daga cikin sakamakon irin tsare-tsare, da manufofi da suka fitar don samar da cigaban Ilimi.

Ta kara da cewa, wannan karon gwamnati ta fitar da tsari wanda ya bam-bamta da wanda suka wuce domin dakile matsalolin da suka addabi ilimi a jihar, wanda hakan zai kawo cigaban fannin ilimi.

A karshe kwamishiniyar ta bayyana jin dadin ta bisa masu shawara da hukumar UNICEF ta tura jihar domin taimaka musu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan