Kungiyar Miyyati Allah Bata Karbi Kudi A Hannun Gwamnati Ba – Inji Ministan Harkokin Cikin Gida

45

Ministan harkokin cikin gida, janar Abdurrahman Bello Dambazau mai ritaya ya karyata batun da ke cewa gwamnatin tarayya ta baiwa kungiyar Miyatti Allah kudi a taron da suka yi garin Birnin Kebbi.

Ministan ya ce wannan batu na bayar da kudi aikin masu yada jita-jita ne, domin a lokacin da ya gudanar da taro da wakilan kungiyar miyatti Allah, babu batun tattaunawa akan kudi ballantana a basu. Wannan wani yunkuri ne na kawar da hankalin mutane daga kan batun kashe-kashe da ake yi a jihar Zamfara.

Janar Dambazau mai ritaya ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyara jihar Zamfara a fadar Sarkin Anka, Alhaji Attahiru Ahmad domin tattauna wa akan batun tsaron jihar.

Ya kara da cewa gwamnati za ta samar da duk tsaron da ake bukata ga manoma domin basu damar yin noma ba tate da sun fuskanci wata matsala ba a damunar bana.

A nasa bangaren, sarkin Anka wanda shi ne shugaban sarakunan jihar Zamfara, ya bukaci gwamnati da ta kara kaimi wajen magance matsalolin tsaro. Ya kara da cewa idan har gwamnatin Tarayya ba ta dauki kwararan matakai ba, to kauyuka da yawa ba zasu samu damar yin noma ba a damunar bana saboda mafi yawancin al’umma sunyi gudun hijira daga garuruwan su kuma mafiyawancinsu mata ne da yara da suka dawo manyan birane.

Sarki Ahmad ya ce , yanzu haka akwai mutane 16,000 da suka yi gudun hijira daga kauyukan su zuwa garin Anka saboda hare-haren yan ta’adda da ya addabe su. Don haka ya yi kira ga jami’an tsaro da su yaki wadannan yan ta’adda da suke boye a kauyukan da aka tsere

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan