Wani sabon doka da sarkin Swaziland ya fitar ya wajabtawa mazan garin auren mace fiye da daya. Ga wanda ya bijire wa dokar, to zai fuskanci fushin hukuma ta hanyar zaman gidan yari.
Sarkin na Swaziland mai suna mai martaba Mswati na uku, ya ce dokar zata taimaka wajen sama wa mata mazajen aure a kasar ta sa, ganin cewa yawan mata ya ninka na maza sosai.
Sarki Mswati ya kara da cewa dokar zata fara aiki ne a watan Yuni mai kamawa na wannan shekara. Sannan, ya bayyana cewa gwamnati a shirye ta ke ta tallafa wa duk mai niyyar auren mata biyar da muhallin zama, da kuma kudin shagulgulan biki.
IHarare, sun kawo rahoton cewa sarkin ya ce hakan shi ne zai zama mafita domin sama wa dinbin yan matan da ke kasar mazajen aure. Sarki Mswati yana auren mata 15 kuma ya haifi ýaýa 25. Ya gaji sarautan daga mahaifinsa wanda ya auri mata 70, ya haifi ýaýa sama da 150.