Alkalin da zai busa wasan karshe na champions

124

An bayyana Damir Skomina a matsayin alkalin wasan da zai jagoranci wasan karshe na gasar zakarun turai da za a fafata tsakanin Liverpool da Tottenham.

Saidai wannan alkalin wasa tarihi ya nuna cewa duk lokacin da zai hurawa Liverpool wasa to basu fiye samun nasara ba.

A nan ma ko tarihi zai maimaita kansa?

Ga jerin wasanni da sakamako da ya jagoranci Liverpool a baya:

A ranar 9/12/2009 ya jagoranci wasa tsakanin Liverpool da Fiorentina inda aka lallasa Liverpool daci 2 da 1.

A ranar 26/2/2015 ya jagoranci wasa tsakanin Liverpool da Besiktas inda aka casa Liverpool daci 2 da 1.

A ranar 28/4/2016 ya jagoranci wasa tsakanin Liverpool da Villarreal inda Liverpool tayi rashin nasara daci 1 da nema.

A ranar 2/5/2018 ya jagoranci wasa tsakanin Roma da Liverpool inda aka caskara Liverpool daci 4 da 2.

Tunda yake jagorantar Liverpool a wasanni sau daya kacal suka taba samun nasara wato wasan da Liverpool ta lallasa Napoli da ci 1 mai ban haushi a ranar 11/12/2018.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan