Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Athletico Madrid kuma dan asalin kasar France ya bayyana cewar a karshen kakar wasa ta bana zai bar kungiyar ta Athletico.
Griezmann dai ya jima yana buga wasa a kungiyar ta Athletico kuma ya kafa tarihi daidai gwargwado a kungiyar.
Griezmann ya buga wasanni 256 a kungiyar ta Athletico inda ya ci kwallaye 133 kuma ya taimaka aka zura kwallaye guda 50.

Ga jerin kofunan da ya lashe a kungiyar:
Ya lashe gasar Europa League guda 1.
Ya lashe gasar UEFA Super Cup guda 1.
Ya lashe gasar Supercopa de España guda 1.
Griezmann ya kwashe shekaru 5 a Athletico saidai an bayyana cewar Barcelona na zawarcin wannan dan wasa.
Turawa Abokai