Ko kun san cibiyoyin ɗaukar jarrabawa da JAMB ta dakatar?

200

Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu, JAMB ta saki wani jerin sunayen Cibiyoyin Gwaji ta Kwamfiyuta, CBT da ta dakatar biyo bayan sakin sakamakon jarrabawar Bai Ɗaya ta Shiga Manyan Makarantu, UTME.

A ranar Asabar ne Ishaq Oloyede, Magatakardar JAMB ya sanar da sakin sakamakon jarrabawar bayan wani dogon jinkiri, yana mai bayyana cewa Hukumar ta riƙe sakamakon ɗalibai 34, 120 sakamakon laifuka da dama.

Ya kuma ƙara da cewa Hukumar na riƙe da sakamako 15, 145 don ci gaba da bincike.

A halin yanzu, JAMB ta wallafa sunayen CBT 22 a faɗin ƙasar nan, inda jihohin Edo, Ekiti, Abia da Nasarawa ke da cibiyoyi mafiya yawa da aka dakatar.

Huɗu daga cikin cibiyoyin dake jerin sunayen suna Edo, yayinda Abia da Ekiti ke da cibiyoyi biyu, kamar yadda yake a cikin kundin dake ƙunshe da cibiyoyin da aka soke ɗin.

A cewar JAMB, an samu cibiyoyin ne da laifuka da dama da suka haɗa da karɓar kuɗaɗen rijista daga ɗalibai fiye da yadda gwamnati ta sa, rashin ɗa’a a wajen yin rijista, da yin jarrabawa ba bisa ƙa’ida ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan