Kotu ta soke naɗin sabbin sarakuna da Ganduje ya yi

27

Wata Babbar Kotun Jihar Kano ta bayyana naɗa sabbin sarakuna da Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abudullahi Ganduje ya yi a matsayin ɓatacce, kuma bai yi ba.

Mai Shari’a Nasiru Saminu ya yanke hukuncin ranar Laraba biyo bayan ƙarar da Onorabul Sule Gwarzo ya shigar, inda yake ƙalubalantar raba Masarautar Kano zuwa gida biyar da Gwamnatin Jihar Kano ta yi.

Kotun ta bada umarnin a dawo yadda ake da, har lokacin da za ta gama sauraron ƙarar.

Dama tuni masu naɗa Sarkin Kano suka shigar da irin wannan ƙara ranar Talata.

Labarai24 ta bada rahoto sabbin sarakunan da suka haɗa da Aminu Ado Bayero, Sarkin Bichi; Alhaji Tafida Abubakar Ila, Sarkin Rano, Ibrahim Abdulƙadir, Sarkin Gaya da; Dakta Ibrahim Abubakar II, Sarkin Ƙaraye.

Muhammad Sanusi II shi zai ci gaba da kasancewa Sarkin Kano.

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan