Mun san ‘yan siyasar dake ɗaukar nayin ta’addanci a Najeriya- Burutai

212

Babban Hafsan Sojin Ƙasa na Najeriya, Laftanar Janar Yusuf Burutai ya danganta yawan aikata laifuka a ƙasar nan da ‘yan siyasar da suka faɗi babban zaɓen ƙasar nan.

Ya ce suna da hujja mai ƙarfi game da ‘yan siyasar dake ɗaukar nayin kashe-kashe, garkuwa da mutane da sauran nau’ukan laifuka.

Burutai ya bayyana haka ne lokacin da yake karɓar Shugaban Kwamitin Sojoji na Majalisar Wakilai a Maiduguri.

“Barazanar Boko Haram tabbas da gaske ne, an yi maganinsu, amma har yanzu suna nan. Ta fuskar hare-haren da suke kai wa wuraren da jami’an soji suke, ‘yan ta’addar suna kan tserewa, amma saboda yadda tsarin ta’addanci yake, sukan yi abubuwa don su nuna cewa fa suna nan da ƙarfinsu.

“Akwai ƙarin hare-hare da muke fuskanta a halin yanzu a Arewa Maso Yamma, Arewa ta Tsakiya da sauran sassan ƙasar nan. Ina son in yadda da cewa bayan kammala manyan zaɓukan ƙasar nan, akwai ‘yan siyasar dake ganin faɗuwarsu a matsayin abin ɗaukar fansa, sukan ɗauki nauyin waɗannan ayyukan ta’addancin, har da ma kashe-kashe, rikici tsakanin manoma da makiyaya.

“A wata ma’anar, akwai tasirin siyasa mai ƙarfi”, in ji Burutai.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan