Home / Addini / DIMBIN FALALAR DA KE CIKIN WATAN RAMADAN

DIMBIN FALALAR DA KE CIKIN WATAN RAMADAN


Watan Azumin Ramadan shi ne wata na tara a lissafin watannin Musulunci, kuma a ciki ne Musulmi a fadin duniya suke gudanar da Azumi na tsawon kwanaki 29 ko 30.

Wannan wata yana dauke da dimbin Falala da albarka da Rahamar Ubangiji Subhanahu Wa Ta’ala. Don haka ya ke da muhimmanci ga al’ummar Musulmi, su gudanar da aiyukan Ibada da neman Lada don samun gafara.

Bugu da kari, watan yana dauke da muhimman abubuwa na tarihin addinin musulunci masu tasiri a rayuwar musulumi baki daya.

Ga kadan daga cikin Falala da watan Ramadan ke dauke da su.

  1. Takawa: Azumi a watan Ramadan yana kara wa al’umma tsoron Allah, da yawaita ibadu da kara kusanci ga Allah. Wannan yana sa karin takawa a zukatan al’umma domin jama’a da dama na barin al’amura na shagaltar duniya su maida hankali wajen neman gafarar ubangiji da neman aljanna.
  2. Tsari: Watan Ramadan yana zama kariya ga al’umma a yayin da Azumi ya ke gudana. Jama’a da dama suna raba kawunan su da aikata aiyuka na alfasha, ko rashin kunya ko rashin mutumci daa dai sauransu. Mutane kan kasance cikin halaye na kwarai a wannan wata mai alfarma. Don haka watan Ramadan yana zama tsari ga mutane daga munanan halaye da dabi’u marasa kyau.
  3. Saukar Da Al-Kur’ani: A cikin wannan wata na Ramadan aka sauke Alkur’ni mai girma, wanda wahayi ne daga Allah SWT zuwa Annabi Muhammad SAW domin ya zama shiriya, da tafarki madaidaici, da Rahama, da Waraka, da Albishir ga masu Imani sannan ya zama gargadi ga wanda suka kafirta. Yana da matukar falala yawan tilawar alkur’ani a cikin wannan wata.
  4. Bude kofofin Aljanna: Ya zo a hadisin Manzon Allah SAW cewa a cikin wannan wata na Ramadan na ne kadai ake bude dukkanin kofofin Ajanna saboda rahamar Ubangiji sannan kuma a rufe dukkanin Kofofin gidan Wuta. Sannan kuma ana daure shedan da daukacin shedanu saboda tsarkake watan.
  5. Daren Lailatul Kadr: Ya zo a cikin Alkur’ani mai girma cikin suratul Qadr inda Allah ya sanar da musulmi baki daya wani dare wanda yafi watanni guda 1000, da mala’iku suke sauka a ciki da Izinin Ubangiji. Daren yana dauke da rahama har zuwa ketowar alfijir, kuma ana so a yi Ibada a cikin sa. Wannan dare ana samun sa, a kwanaki goma na karshen watan Ramadan. Wanda ya yi dace da samun wannan dare zai samu Rahamar Allah SWT.
  6. Al-Rayyan: Ya zo a hadisin Manzon Allah SAW cewa akwai wata kofa a Aljanna mai suna Al Rayyan. Babu mai shiganta sai wanda ya ke azumi. Wannan Falala yana kara kwadaitar da al’umma musulumi wajen bada kaimin yin Azumi a watan Ramadan saboda su sami albarkar da ke cikin wannan Kofa ta Al Rayyan a lahira.
  7. Ciyar da Mai Azumi: Yana da matukar lada ciyarwa a cikin watan Ramadan. Duk wanda ya ciyar Allah zai bashi ladan wanda ya ciyar ba tare da an rage wa wanda aka ciyar ladan azumin shi ba. Ana ciyarwa a watan Ramadan ta hanyoyi da dama kamar Sadaka, da kyauta na kayan abinci danye, ko kuma dafaffe, ko kuma bada kudin kayan abincin ga wanda suke da bukata.
  8. Sallah Tarawee: A cikin watan Ramadan ne ake gudanar da sallolin Tarawee. Sallah Tarawee Salloli ne da ake yi raka’a goma bayan Sallar Isha, sannan kuma ana yin wasu raka’a goman cikin karshen dare daf da lokacin sahur a kwanaki goma na karshen watan domin neman falala da gafarar Ubangiji.
  9. Umrah: Ya zo a hadisin Manzon Allah SAW cewa, duk wanda ya yi Umrah a watan Ramadan to yana da lada kamar ya yi aikin Hajji tare da Manzon Allah SAW.
  10. Karin Lafiya: Yin Azumi watan Ramadan yana taimakawa jikin Dan Adam ya samu karin kuzari, da damar tsaftace kansa daga abubuwa rasa amfani ga jikin.

A karshe, yana da kyau mu sani, watan Ramadan yana kara kusanci a tsakanin al’umma musulmi, yan daidaita tsakaninsu, yana sanya tausayi da jinkai, sannan yana saka aikata aiyuka na alkhairi da kyawawan dabi’u. Allah ya bamu ikon samu falalar da ke cikin wannan wata, ameen.

About Amina Hamisu Isa

Check Also

Fahimta Fuska: Addinin Musulunci ya amince da ‘Halaccin’ yin shirin Fim – Sheikh Ibrahim Khalil

Shugaban majalisar malaman jihar Kano, kuma tsohon mai bai wa gwamna Ganduje shawara a kan …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *