Ko kun san waɗanda suka raka Buhari Filin Jirgin Sama don tafiya Saudiyya?

196

Ranar Alhamis ne Shugaba Muhammadu Buhari ya tashi zuwa Saudiyya daga Filin Jirgin Saman Ƙasa da Ƙasa na Nnamdi Azikiwe dake Abuja.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya bada rahoton cewa jirgin dake ɗauke da Shugaban Ƙasar da muƙarrabansa ya tashi ne da misalin ƙarfe 11 na safe.

Waɗanda suka raka Shugaban zuwa Filin Jirgin don yin ban-kwana da shi sun haɗa da Shugaban Ma’aikatansa, Abba Kyari; Ministan Babban Birnin Tarayya, Mohammed Bello; Muƙaddashin Babban Sifeton ‘Yan Sanda, Muhammed Adamu da sauran jami’an gwamnati.

Rahoton NAN ya ce tafiyar Shugaban Ƙasa zuwa Saudiyya ta biyo bayan gayyatar da Sarkin Saudiyya kuma Mai Kula da Masallatai Biyu Masu Tsarki, Salman Bin Abdul’aziz ya yi masa.

Wata sanarwa da Mataimaki na Musamman ga Shugaba Ƙasa Kan Kafafen Watsa Labarai, Garba Shehu ya fitar ranar Laraba ta ce Shugaba Muhammadu Buhari zai yi Umara yayin zaman nasa a Saudiyya.

Lokaci na ƙarshe da Shugaba Buhari ya yi Umara shi ne a watan Fabrairun 2016.

Umara dai ibada ce da za a iya yin ta kowane lokaci a shekara, kuma ba wajibi ba ce, amma tana da lada sosai musamman a watan Ramadan.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan