Kotun Ƙoli ta sa ranar da za ta yanke hukunci game da rikicin APC a Zamfara

182

A ranar Alhamis ne Kotun Ƙoli ta sa ranar 24 ga watan Mayun da ake ciki a matsayin ranar da za ta yanke hukunci game da ƙarar da aka ɗaukaka a gabanta kan rikicin zaɓukan fitar da gwani na jami’yyar APC a jihar Zamfara, wanda ya samar da ‘yan takarar da jam’iyyar ta tsayar a babban zaɓen da ya gabata.

Muƙaddashin Alƙalin Alƙalan Najeriya, Mai Shari’a Tanko Muhammad ne ya jagoranci alƙalai biyar da suka saurari ƙarar ranar Alhamis.

Babbar Kotun Tarayya dake Abuja da Babbar Kotun Jihar Zamfara sun bada hukunce-hukunce biyu masu cin karo da juna game da ko jam’iyyar APC ta gudanar da sahihan zaɓukan fitar da gwani ko kuma a’a.

Haka kuma, Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Abuja da Sokoto su ma sun yanke hukunce-hukunce masu cin karo da juna.

Tsagin Gwamna Abdul’aziz Yari, wanda yake samun goyon bayan shugabancin jam’iyyar na ƙasa shi ya fitar da ‘yan takarar da suka shiga zaɓe a jihar, ya kuma dage kan cewa jam’iyyar ta gudanar da zaɓukan fitar da gwani sahihai a jihar, tsagin Sanata Kabir Marafa kuma na cewa ba a gudanar da zaɓen fitar da gwani ba a jam’iyyar ta APC

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan