Garba Shehu ya bayyana inda Buhari yake a Saudiyya

49

A ranar Juma’a ne Shugaba Muhammadu Buhari ya sauka a Makka bayan ya bar Madina, inda ya fara aikin Umararsa gadan-gadan.

Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa Kan Kafafen Watsa Labarai, Garba Shehu ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Asabar da safe.

“Bayan sallar La’asar a Masallacin Annabi Mai Tsarki a Madina, an jagoranci Shugaban zuwa Kushewar Annabi Muhammadu inda ya yi wa ƙasar nan, iyalansa da kansa addu’a.

“Gwamnan Lardin Madina, Yarima Faisal Bin Salman Bin Abdul’aziz Al-Saud shi ya raka shi zuwa Filin Jirgin Saman Ƙasa da Ƙasa na Mohammed Bin Abdul’aziz dake Madina.

Mista Shehu ya ƙara da cewa Gwamnan Lardin Makka, Yarima Khalid Bin Faisal Al-Saud shi ya karɓi Shugaban a Makka.

Daga cikin waɗanda suka tarbi Shugaban akwai Jakadan Najeriya a Saudiyya, Isa Dodo, Darakta Janar na Hukumar Leƙen Asiri ta Ƙasa, Ahmed Rufa’i Abubakar da jami’an ofishin Jakadamcin Najeriya dake Jidda.

“Bayan tarbar Shugaban Ƙasar, kai tsaye sai ya tafi don fara aikin Umara ranar Juma’a da yamma”, in ji Garba Shehu.

Ranar 16 ga watan Mayu ne Shugaba Buhari ya bar Abuja zuwa Saudiyya biyo bayan gayyatar da Sarkin Saudiyya kuma Mai Kula da Masallatai Biyu Masu Tsarki, Sarki Salman Bin Abdul’aziz ya yi masa don gudanar da ibadar Umara.

Shugaban, wanda ake sa ran dawowarsa ƙasar nan ranar 21 ga watan Mayu, ya yi Umara ta ƙarshe ne a watan Fabrairu, 2016.

Umara dai ibada ce ba ta wajibi ba, amma mai tarin lada da ake gudanar da ita a Makka a kowane lokaci a shekara.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan