Atiku ya buƙaci wata hadimar Buhari ta biya shi Naira Miliyan 500 sakamakon ɓata masa suna

216

Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP a zaɓen shekara ta 2019, Atiku Abubakar, ya buƙaci hadimar Buhari, Lauretta Onochie ta biya shi Naira Miliyan 500 tare da neman afuwarsa a rubuce sakamakon ‘yaɗa ƙarya da za ta iya zubar masa da mutunci’.

A wata wasiƙa da aka rubuta wa Onochie kuma lauyan Atiku, Mike Ozekhome, SAN, ya sanya wa hannu, tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar ya fusata da rubutun Onochie a Twitter, inda ta ce jami’an tsaron Haɗaɗdiyar Daular Larabawa, UAE na neman Atiku ruwa a jallo.

Atiku ya ce bai taɓa kasancewa a wani jerin sunaye da jami’an tsaro ke nema ba, ya kuma ƙalubalanci Onochie da ta kawo hujja don tabbatar da zarginta.

Ya ce zai shigar da Onochie ƙara ta ba shi Naira Biliyan 2, bisa cin mutumci ta Intanet idan ta kasa cika buƙatun da ya gindaya.

“Mun samu izinin wanda muke karewa, mu buƙaci, saboda haka yanzu muna buƙatar waɗannan abubuwa masu zuwa daga gare ki: Ki wallafa, tare da miƙa rubutacciyar janyewa da neman afuwa bisa wancan rubutu dake ɓata suna a jaridun ƙasar nan dake zagayawa guda shida, da kuma jaridar waje guda ɗaya, da kuma dukkan dandalin sada zumunta inda aka yi yi wancan rubutu.

“Cewa ki biya wanda muke karewa ta kamfanin, jimillar Naira Miliyan 500, daidai da irin cutar da aka yi masa, don rage raɗaɗin zubar masa da mutunci da rubutunki na zubar da mutunci ya jawo.

“Ki sani cewa idan ki ka kasa ko ki ka ƙi biyan wannan buƙata tamu da ba ta wuce ƙima ba cikin sa’o’i 48 daga kwanan watan wannan wasiƙa, za a tilasta mana mu ɗauki cikakken matakin shari’a a kan ki ba tare da dawowa wajenki ba.

“Idan muka shigar da wannan ƙara, za mu buƙaci ki ba mu jimillar Naira Biliyan 2, daidai da misalin cutarwa rubutun ya jawo”, in ji wasiƙar.

Onochie, wadda ta kasance hadimar Buhari tsawon shekara uku ta saba caccakar mutanen dake sukar Shugaba Buhari.

A bara, ta siffanta Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya a matsayin, CAN ‘a matsayin ‘Ƙungiyar Kiristoci ta tsutsotsi’, bayan da suka ce Shugaba Buhari bai yi wa Kiristoci adalci ba.

Haka kuma, CrossCheck Nigeria- gamayyar kafafen watsa labarai 15 ta bankaɗo ta da laifin yaɗa wasu hotuna na yaƙin neman zaɓen PDP, inda aka nuna an tara abinci da kuɗi ana raba wa mahalarta taron.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan