Abinda zan yi bayan ƙirƙirar sabbin masarautu- Ganduje

262

Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abudullahi Umar Ganduje ya tabbatar da cewa sabbin masarautu huɗu da ya ƙirƙira fa sun zo kenan, yana mai nanata cewa an ƙirƙiro su ne da kyakkyawar niyya, ba don a ci mutuncin wani ko gungun wasu mutane ba.

Ya bayyana haka ne ranar Lahadi, inda ya nanata cewa Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ba fa shi kaɗai ne Sarki Mai Daraja ta Ɗaya ba yanzu a jihar.

Da yake goyon bayansa wajen gudanar da sabbin masarautun, ya ƙalubalanci kansa da kansa, inda ya ce: “A matsayina na ɗan dagaci, ya za a yi in yi wani abu da zai ɓata abinda muka gada kaka da kakanni”?

“Idan ka ƙirga kakannina, kusan goma daga cikinsu duk dagatai ne, har zuwa mahaifina. To, nakan kasa fahimta idan mutane suka ce gwamnatina tana son cutar da wannan masarauta mai daraja”, in ji Gwamna Ganduje.

Gwamnan yana waɗannan bayanai ne lokacin da ya je ta’aziyya Fadar Sarkin Rano bisa rasuwar uwargidan Mai Shari’a Wada Rano, Hajiya Khadija Wada, bayan ziyartar gidan su marigayiyar, duka a ƙaramar hukumar Rano.

Ya ƙara da cewa lokacin da yake rattaba hannu ga Dokar ta ta ƙirƙiro Masarautun Rano, Bichi, Ƙaraye da Gaya, ya bayyana a fili cewa maƙasudin samar da sabbin masarautun shi ne su kawo ci gaba kusa ga mutanen dake karkara.

Ya ce bayan rantsar da shi a wa’adin mulki na biyu, “Za mu zo sabuwar kuma hanya ta zamani don ci gaban jiharmu. Wannan dabara, za ta haɗa a kusa-kusa, Majalisun Sarakunanmu. Dalilin da yasa muka fahimci ya kamata a samar da waɗannan Majalisun Sarakunan kenan”.

A cewar Ganduje, akwai buƙatar gwamnatinsa ta ta tashi Masarautar Kano daga bacci.

Ya umarci Sarkin Rano da ya hukunta Hakimin Bebeji wanda aka ce ya ajiye aikinsa a wani salo na rashin nuna yadda da Sabbin Masarautun, yana mai ƙarawa da cewa: “Idan da gaske ne ya yi murabus, Sarkin zai iya aikawa da wakili a can kafin naɗa Sabon Hakimi”

Gwamnan ya bayyana gamsuwa da wasu matasan Bebeji suka yi zanga-zanga don nuna goyon bayansu ga ƙirƙirar Masarautar Rano, ya kuma yi kira da a tsige Hakimin Bebeji sakamakon rashin zuwansa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan