Mutanen Badarawa Sun Yi Arangama Da Barayin Shanu Sun Dawo Da Nasara
Jama’ar garin Badarawa, sun yi arangamar fito-na-fito da wani gun-gun barayin shanu, a daren jiya.
Arangamar ta biyo bayan kokarin ‘yan ta’addan na afkawa garin.
Mutanen garin sun yi nasarar kashe barawo biyu. A daya bangaren, barayin sun kashe mutum daya cikin mutanen garin, sannan sun kore wasu dabbobi da ke kiwo a fadamar garin.
Garin Badarawa da ke karamar hukumar mulkin Shinkafi, na daga cikin garuruwan da ke fuskantar hare-haren ta’addanci.
Daga Abdurrahman Abubakar Sada
Turawa Abokai