EFCC ta bayyana sunan wani ƙasurgumin ɗan siyasa da take bincike

166

Hukumar Hukunta Masu Yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati, EFCC ta tabbatar da cewa tana binciken Gwamna Rochas Okorocha na Jihar Imo.

Muƙaddashin Shugaban Hukumar ta EFFC, Ibrahim Magu ya tabbatar da haka lokacin wata keɓantacciyar ganawa da Channels Television a Landan.

Da aka tambaye shi ana ci gaba da bincike game da Gwamnan, sai ya bada amsa da cewa “tabbas”.

“Ba shakka, muna yin wasu ‘yan bincike-bincike nan da can. Kusan muna binciken kowa”, in ji Shugaban na EFCC.

Ya ce dole sai Hukumar ta kai wani mataki kafin ta iya bada wasu bayanai game da wani bincike da ake kan yi.

Mista Magu ya ce hakan ya zama wajibi don guje wa duk wani abu da zai iya jefa ko ya kawo tarnaƙi da yadda ake yin binciken.

A cewarsa, Gwamna Okorocha yana ɗaya daga cikin mutane da dama da Hukumar ke bincika.

Shugaban na EFCC ya ce koda yake yana sane da rahotannin binciken a kafafen sada zumunta, bayanan da suke hannun Hukumar daban suke da abinda yake hannun jama’a.

Amma ya ƙi ya bayyana bayanan.

Mista Magu ya je Birtaniya ne don ganawa da masu bincike waɗanda za su taiamaki Najeriya wajen warware matsalolin halatta kuɗin haram da sauran laifukan mu’amala da kuɗi.

A kwanan nan ne Gwamna Okorocha ya ce yana ƙarƙashin komar EFCC, yana mai cewa shi ne gwamnan da EFCCn ta fi bincika a ƙasar nan.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan