Adadin kuɗaɗen manyan ayyuka da Gwamnatin Tarayya ta fitar- Ministan Kasafin Kuɗi

50

Gwamnatin Tarayya ta saki sama da Naira Triliyan 4.33 a shekaru uku da suka gabata ga Ma’aikatu, Sashe-sashe da Hukumomin Gwamnati don gudanar da manyan ayyuka.

Ministan Kuɗi da Tsare-tsaren Ƙasa, Udoma Udo Udoma ya bada alƙaluman a yayin wani taron manema labarai game da aikace-aikacen Ma’aikatar da hukumominta a ƙarƙashin shugabansa.

Da yake bada yadda jimillar kuɗin suke, Ministan ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya, ta Ma’aikatar Kuɗi ta iya sakin Naira Triliyan 1.2 a ƙarƙashin kasafin kuɗin 2016 don gudanar da manyan ayyuka.

A shekarar kuɗi ta 2017, Ministan ya ce an fitar da Naira Triliyan 1.2, yayinda zuwa 8 ga watan Mayu, 2018, an saki Naira Triliyan 1.55 don gudanar da manyan ayyuka a kasafin kuɗin 2018.

Ya ce an mayar da hankali ne a kan manyan ayyukan don farfaɗo da tattalin arziƙi biyo bayan matsin tattalin arziƙi da ƙasar nan ta fuskanta a 2016.

Ya ce: “Wata muhimmiyar dabara da muka ɗauka don fita daga matsin tattalin arziƙi shi ne duba yadda za a farfaɗo da tattalin arziƙin”.

“Shi yasa muka ƙara kasafin kuɗin manyan ayyuka daga kaso 16.1 cikin ɗari a 2015 zuwa kaso 30.2 cikin ɗari a 2016, kaso 31.7 cikin ɗari a 2017, kaso 31.5 cikin ɗari a 2018 da kaso 26 cikin ɗari a 2019. Kuma, mun iya ƙara yawan kuɗaɗen manyan ayyuka”, in ji Mista Udoma.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan