Gwamnan Rivers ya tumɓuke wani babban basarake a jihar

228

Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Ezenwo Wike ya amince da ƙwace Takardar Shaidar Zama Sarki da Sandar Mulki daga Mai Martaba, Cif Frank Noryaa, Gbenemene Baabe.

Simeon Nwakaudu, Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Kan Kafafen Watsa Labarai na Intanet ya sanar da haka jiya a wata sanarwa.

A cewar sanarwar, tumɓuke Mai Martaba Noryaa da gwamnati ta yi ya biyo bayan samun sa da hannu a harkokin tsafi a masarautar tasa.

“An kuma samu basaraken da laifin ajiye matsafa, abinda ya haifar da rashin tsaro a yankin”, in ji Mista Nwakaudu.

Sanarwar ta jiyo Gwamnan yana cewa: “Gwamnatinsa a shirye take wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a dukkan faɗin jihar”.

Gwamnan ya gargaɗi sauran sarakunan gargajiya da jami’an gwamnati da samun su da laifin samar da rashin tsaro, yana mai cewa za su fuskanci cikakken fushin hukuma.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan